✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko cin namijin goro na da illa ga lafiyar mutum ko amfani?

Ko cin namijin goro na da illa ga lafiyar mutum ko amfani? Ya ya kamata a rika cinsa?   Amsa: To namijin goro kamar dan…

Ko cin namijin goro na da illa ga lafiyar mutum ko amfani? Ya ya kamata a rika cinsa?

 

Amsa: To namijin goro kamar dan uwansa ba abinci ne da akan sa a gaba a ci a koshi ba, a’a ana cinsa ne jefi-jefi kamar kayan nishadi, a wurin biki ko suna da sauransu. To binciken masana hada magunguna ya nuna cewa namijin goro na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwa da suka fi yawaita bincike a kansa, kuma sun gano yana da amfani wajen kashe wasu kwayoyin cuta, amma dai har yanzu ba su hada shi a matsayin gundarin kwayar magani ba tukuna. Sun kuma yi binciken ko zai iya lahani ga wani sashe na jiki kamar hanta da koda idan an ci shi, amma ba su gano ba. Wannan kusan ke nan zai zama kalubale gare su da su hanzarta samar da wata kwayar magani daga wannan dan itace mai matukar amfani kamar yadda wata cikinsu ta yi maganin maleriya da darbejiya.

 

Ni na kan yi fama da ciwon kai da dan zazzabi musamman idan na shiga rana. Ko me ke sa haka?

Daga Fiddausi Ahmad da Abu Ahmad, Zaria

 

Amsa: E, rana za ta iya sa ciwon kai ita kanta, saboda tana dukan kwanyar ka, za ma ta iya sa suma, wanda akan kira bugun rana, amma ba za ta sa zazzabi ba. Idan aka ji zazzabi in an shiga rana dama can akwai shi a jiki, sabanin ciwon kai wanda rana ita kanta za ta iya saka shi. Don haka mai zazzabi ya je asibiti a duba sababin zazzabin, mai ciwon kai kuma ya rage shiga rana.

 

Mene ne ke sa wasu idan ruwa ya dake su sai sun yi zazzabi?

Daga Nasiru Kainuwa, Hadejia

 

Amsa: Ka san a jikinmu musamman kofofin hanci da makoshi akwai kwayoyin cuta a makale a saman fata wadanda ba sa kawo cuta, amma da wani abu ya faru kamar shigar sanyi ko bushewar wurin, suka samu suka shiga jiki ta wannan kafar, wato makoshi da hanci, sai a fara jin zazzabi da mura. Wadannan kwayoyin cuta yawanci na birus ne. Abubuwan da kan jawo su shiga jiki kuma har da dukan ruwan sama, domin shi ma dukan ruwan sama kan sa kofofin su yi sanyi, magudanan jinin wurin su matse, a samu kafa. To ka ji dalilin cewa kwana daya zuwa biyu idan ruwa ya daki wasu mutanen suke samun mura da zazzabi. Wani lokaci ba sanyin ruwan sama ba, har da sanyin na’urar sanyaya wuri da ta fanka, da ma sanyi na gari.

 

Ni na kasance ina yawan yin jiri. Ko me ke kawo hakan?

Daga Murtala kwalli

 

Amsa: Akwai abubuwa da dama masu sa jiri, kuma duk ba na lafiya ba ne, don haka jiri alama ce ta ciwo sai ka je a binciki dalili kafin karamin abu ya zama babba.

 

Idan na kai azumi na sha ruwa musamman idan mai sanyi ne, sai na ji kamar kaina na juyawa. Shin wannan matsala ce?

Daga Ibrahim Rabilu, Zamfara

 

Amsa: A’a ba matsala ba ce. Duk wani dan jiri ko juyin kai yayin cin abinci ko shan wani abu da bayan cin ko shan da ‘yan mintuna ba matsala ba ce, saboda a lokacin jiki na yanko wani kaso na jini daga kwakwalwa ya kai shi ciki domin a yi saurin tsotse abinda aka ci ko aka sha din. Ba kowa ne dai kan samu irin wannan ba, kai ma watakila saboda ka ce azumi ka yi, wato ka dade ba abinci a jikinka shi ya sa watakila ka ji haka. Amma duk wasu sauran nau’uka na jiri da juyin kai banda wannan ba na lafiya ba ne.

 

Me ke kawo yawan saurin bugawar zuciya? Ko da a yau na ji.

Daga Suraj Y. Zamfara

 

Amsa: To kai ma dai a takaice, da yake an sha amsa irin wannan tambaya, abin da za a ce maka shi ne ba lafiya ba ne ka ji irin wannan saurin bugun zuciya. Idan ka samu ka ga likita ido-da-ido ya duba ka. zai zayyana maka dalili ya kuma gaya maka mafita.

 

Ina fama da mura mai tsanani da toshewar hanci da majina. Ina shan magungunan asibiti tsawon sati biyu amma ba sauki. Shi ne na ke neman shawara.

Daga Hassan Muhammad, Lagos

 

Amsa: Kana shan maganin asibiti amma ga alama saya ka yi a kyamis ka ke sha. Dama ai ko a talla kana jin masu magungunan suna cewa idan bayan kwana biyu baka ji sauki ba, ka tuntubi likitanka. Ga shi kai har an yi sati biyu baka ji sauki ba, baka kuma tuntubi likitanka ba. Don haka a nan wurina shawara tunda ban ganka ba, ka je likita ya ganka.

 

Ko farin wata yana sa mura? Domin ni da an yi farin wata zan ji mura. Ko hakan na nufin ina da wata matsala?

Daga Abubakar S., Mai’Adua

 

Amsa: A likitance babu alaka tsakanin cikar wata da mura, amma watakila a ilmin halayyar dan Adam akwai. Domin bincike ya dan nuna masu ilmin sanin halayyar dan Adam ta Psychology sun zurfafa bincike a wannan fanni, ba likitoci ba. Mu a likitanci canjin yanayi ne muka alakanta da cutuka irinsu mura.

 

Duk lokacin da na ci abinci mai yawa ko mai nauyi sai na ji cikina na ciwo musamman idan na kwanta. Mece ce mafita?

Daga Yunusa I. Ibrahim

 

Amsa: Watakila cikin naka ne yake maka nuni da cewa fa ka bi a hankali, don ba ya so ka cika shi fam. Don haka ka gode Allah ka godewa cikin naka, tunda ga alama idan ka ci kadan ba ya maka ciwo.

 

Ni idan na kwanta barci wasu lokutan da dare na kan yi fitsarin kwance. Ko hakan matsala ce?

Daga Isma’il, Lagos

 

Amsa: kwarai kuwa Mallam Isma’il babba da fitsarin kwance matsala ce sosai ma kuwa. Ka daure ka nemi likitan mafitsara ya gan ka.

 

Mene ne maganin kaikayin gaba ne? Domin na yi magani na yi magani, amma a banza.

Daga dahiru S.M., Abuja

 

Amsa: To ko kai ma sai ka nemi likitan mafitsarar ne a babban asibiti, ya duba ka ya ga mene ne ke jawo maka wannan kaikayi.