A wannan lokaci saboda rashin daraja da kima da malamin makaranta ke da shi har ta kai in ana lissafin ma’aikacin gwamnati za a ji an ce ma’aikaci da malamin makaranta, sannan kuma ko neman aure malami ya je za ka ga ’yan matan da iyayen suna masa kallon wani mara kima, inda suke ganin kamar diyar su ba za ta samu walwala da more rayuwa mai tagomashi ba.
Babban abin da ke kara dakushe kwazon malamin makaranta shi ne, rashin kula da su, ta hanyar ba su dama da kwarin gwiwa don zurfafa ilimin su, musamman malaman da suke da takardar shaidar malanta da makamantan su, tunda an kai wani zamani in har malami ba shi da takardar digree ba zai rike wani matsayi ba, duk kwarewar sa zai ci gaba da zama a matsayin sa na mai koyarwa.
Akwai malamin da na san ya koya man sama da shekara 20, kuma na san yana daga cikin kwararrun malaman mu, ban manta gudunmuwar da ya ba ni har ya zama silar inda na kai a yanzu, amma abin mamaki sai ga shi na gan shi a jami’a a matsayin dalibi, wanda da farko da na gan shi na dauka ko koyarwa yake yi.
Kada fa mu manta a zamanin da ya wuce iyayen mu da sauran magabata, hatta abincin da za su ci a makaranta ana ba su balle ka yi maganar tufafin makaranta (uniform) da kayan karatu, amma saboda a wancan lokacin akwai doka da da’a, kuma ba cin hanci da rashawa ya sa ake samun ingantaccen ilimin.
Idan muka yi la’akari da irin manufar da gwamnatin mu ke da shi, musamman a nan jihar Katsina, cewar ba za ta biya wa kowane dalibi kudin jarabawa ba, har sai ya zana jarabawar cancanta (mock), shi ma abin la’akari ne da ba ta hanzari, duk da masu adawa da hakan na ganin yin hakan zai sa a kara samun yawaitar matasa masu ragaita a hanya ba karatun, balle aikin yi.
Amma hakkin waye tabarbarerewar ilimin?
Kamar yadda na ambata a baya kowane bangare na da rawar da yake takawa don ingantawa ko akasin haka.
1- Iyaye su ne ginshikin samar da al’umma tagari, kuma makaranta ta farko da yara za su samu nagartattar tarbiyya da ilimi mai amfani. Sai dai matsalar yanzu za ka samu da dama daga cikin iyaye suke tsoron ‘ya’yan su, ta yadda za ka ga suna aikata abin da suka ga dama ba su kwaba musu.
2- Gwamnati, ita ce uwa ma-bada mama, wadda ke da doka, kuma ya kamata a ce tana sanya ido akan rayuwar matasa, sannan ta tabbatar duk matsalolin da aka ayyana a cikin makarantun nan da abin da ya shafi ilimin baki daya ta yi kokarin daukar matakan aiwatar da su.
3- dalibai, a nan dalibai (yara) ya kamata su yi wa kan su fada, su zama nagari, domin su ne shugabannin gobe, kuma su sani jahilci da rashin da’a ba inda zai kai su, sai mummunan karshe.
daukacin masu ruwa da tsaki mu tashi tsaye, don ganin an gudu tare, an tsira tare.Hukuma kuwa ta sani hakki ne Allah ya dora mata na al’ummar ta, kuma ranar gobe sai Allah ya tambaye su akan nauyin da ya ba su.
Mu kuma al’umma hakkin gwamnati ne akan mu in ta yi abin da ba daidai ba, mu nuna mata ta hanya mai kyau, amma zage-zage da cin mutunci ba inda zai kaimu.
Sai mu ji tsoron Allah da fatan Allah ya yi mana jagora, ya ba shugabannin mu juriya da karfin gwiwar jagorantar mu bisa adalci.
Sanusi Hashim Abban Sultana [email protected]. Mai sharhi akan al’amurran da suka shafi yau da kullum daga Jihar Katsina