✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ba da ilimi kyauta na kawo tabarbarewarsa? (1)

A wannan karon ina son in yi magana ne akan abin da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya a wannan zamani da muke ciki…

A wannan karon ina son in yi magana ne akan abin da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya a wannan zamani da muke ciki na tababarewar ilimi, tunda in muka duba a lokutan baya na iyaye da kakanni ilimi shi ne abin da ya fi komai mahimmanci. Sanin kowa ne wasu daga cikin Gwamnonin Jihar Arewa sun dauke nauyin karatun yara, inda ya zama kyauta gami da biyan kudin jarabawar shaidar gama makarantar gaba da Firamare.

A daidai wannan hali da ake ciki a wadannan shekaru, kuma sai aka yawaita samun faduwar jarabawar, wadda hakan yake jaza wa kaso mafi yawa daga cikin dari ba su samun cancantar wucewa makarantar gaba.
A irin wannan lokaci ne kuma masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimin da masu sharhi da sauran gama garin mutane ke ta tafka mahawara akan dalilan da suka sa ake samun koma baya.
A duk lokacin da matsala ta jibinci bangarori da dama bisa adalci ba za ka danganta ta ga wani bangare guda ba kai tsaye, don kuwa dole ne kowane sashe da irin rawar da zai taka a samu inganci, haka a wani bangaren zai iya taka wata rawar da za ta iya kawo tawaya a wannan bangare.
Wannan matsala ta zama abin tafka muhawara a majalisun shan shayi da sauran majalisu, inda wasu ke ganin cire tallafin shi zai inganta ilimin yayin da wasu ke da ra’ayin rashin kular gwamnatin ne ga harkar ilimin ya kawo tabarbarerewar tasa.
Ko shakka babu sanya hannun gwamnati ba karamin tasiri yake yi ba, in muka duba yanayin tattalin arzikin da muke ciki wanda da dama ba za su iya biya wa ‘ya’yan su wadannan makudan kudi ba. Amma ina matsalar take; Sai mu koma shekarun baya da kuma farkon zuwan dimokuradiyya,
1- Ga duk wanda ya yi rawuwa a wadancan lokutan, kuma yana zuwa makaranta na san da cewar in har yaro ya bari karfe bakwai da rabi (7:30) ta yi an fara taron jawabi ga dalibai, ke nan sai dai yaro ya koma gida, ko kuma ya bari in an fito tara sannan ya shiga.
A yanzu za ka samu karfe tara (9:00) lokacin yara ke tafiya zuwa makaranta, kuma ba wani mataki da hukumar wadannan makarantu ko gwamnati ke dauka a kan wannan mummunar dabi’a. Abin da ya sa nace ba a daukar mataki, yadda abin ya zama ruwan dare kuma sai ci gaba yake.
2- Yadda malamai suka yi karanci, ta yadda yaro zai iya zuwa makaranta har ya koma gida bai wuce malami guda ya shiga ajin su ba.
Amma a wancan lokacin da nike magana, ni na san shugaban makarantar mu (principal) da muna aji daya za ya shigo in ba malami, ya tambayi abin da muke da shi ya dauko alli ya koya mana. Haka za ka ga shugabannin makarantun suna zagaye da littafin su, su ga wane malami ne ba ya nan su dauki sunan sa. A yanzu saboda karancin malaman ba yadda za a yi haka dalibai za su zauna su yi hirar su, su tashi zuwa gida ko wajen kwanan su.
3- A wancan lokacin makarantun kimiyya da kere-kere (science and technical) ana zaben dalibai ne bisa cancanta su zana jarabawar share fagen shiga, ba tare da iyaye sun samar wa ‘ya’yan su ba, ta hanyar saya musu koda kuwa ba su cancanta ba.
4- A wancan lokacin za ka ga makarantu ana koyar da sana’o’in hannu (Local Craft), sai kuma makarantun kere-kere za ka ga duk wadansu aikace-aikacen da suka jibinci wani sashe daliban wannan sashe ke aiwatar da su. Amma yanzu da dama in ka zagaya za ka samu wadannan bangarori da na ambata ba sa aiki.
5- Rashin kunya da alfasha da suka yawaita a tsakanin daliban, wasu lokutan ma har da malaman, wanda hakan ya sa da dama daga cikin iyaye sun fitar da ‘ya’yan su daga makarantun don gudun kada tarbiyar su ta gurbata, wanda a can baya aal’amarin bai munana haka ba. 6- Muna tattaunawa da wani malamina akan wannan matsala sai ya ce mani shi a tunanin sa rashin karfafa masu bibiyar halin da makarantun (inspectors) ke ciki na daga cikin dalilan da suka jefa ilimi wannan hali, ta yadda inda za a karfafa su, zai kara karfafa malaman, domin sun san cewa ana bibiyar aikace-aikacen su.
7- A baya na yi rubutu akan yadda gwamnati za ta bunkasa ilimi, wanda ban fito kai tsaye na ba ta shawara akan ta kyautata walwala da jin dadin malaman, amma a kaikaice na nusantar da ita akan hakan, wanda hakan ya sa nayi ta samun kiraye-kiraye da kalubale daga su kan su malaman.
A wancan lokacin kowa na sha’awar malanta, saboda darajar da take da ita da muhimmancin da aka ba ta, wanda in ka duba tarihin magabatan mu kusan kowane sai da ya fara taka wannan mataki kafin ya wuce na gaba.
A wannan lokaci malamin makaranta shi ne koma bayan cikin al’umma inda za ka ga mafiya yawan matasan da ke cikin harkar suna yi ne don kawai su samu damar samun tallafi don zurfafa karatun su, wanda da zarar sun kammala sai su tsallake don neman wani aikin wanda suke ganin ya fi tsoka.

Sanusi Hashim Abban Sultana [email protected]. Mai sharhi akan al’amurran da suka shafi yau da kullum daga Jihar Katsina