✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ba a Najeriya Ashigashiyar take ba?

Salam. Aminiya don Allah ku isar min da kokena a madadin kauyen Ashigashiyar zuwa a Sanata Ali Ndume da dan majalisa Hon. Peter Biye da…

Salam. Aminiya don Allah ku isar min da kokena a madadin kauyen Ashigashiyar zuwa a Sanata Ali Ndume da dan majalisa Hon. Peter Biye da Gwamna Kashim Shettima da dan majalisar Jiha da Shugaban karamar Hukumar Gwoza, tunda aka koma tsarin mulkin dimokuradiyya ba a samu ci gaban komai ba, hasali ma sai dai ci baya, ta kowane bangare a Ashigashiya. Fara da hanya da rowan sha da wutar lantarki da ilimi da ayyukan yi. Haba!! Sai ka ce ba a Najeriya muke ba. Daga Baba Muhammad, Abuja 08084771999.

Sakonnin waya

Ina Sanata Sadik ’Yar’aduwa ya shige?

Mu al’ummar Jihar Katsina muna cigiyar Sanata Sadik Yar’aduwa ! Domin tunda kotu ta tabbatar masa da kujerar sa, har yanzu ba zuwa ba aike, mun rasa ruwan da ya ci mana shi, aikin kwandala daya ba mu gani, daga gare shi ba ! Saboda haka mu al’ummar Jihar Katsina ka da Allah maimaita mana irin wannan shugabanci. Daga Haruna Muhammad Katsina. 07039205659.

Alhamdulillahi Kanawa
Wuju-wuju nan tare da raba goro dan ujile ga ’yan acaba, fatanmu Allah ya akre kara zaben da za mu yi da na sani. Daga Mudassir Muhammad Kano Tofa. 08051964333.

Najeriya ta tawaya
Cika shekaru 53 da samun ‘yancin kasata Najeriya, ba wani cigaba da muka samu sai tauyema muna hakkokinnu, da mulkin kama karyar da yafi na Turawan Yamma. Daga Abdulmalik Saidu Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

Ga Yariman Bakura
Aminiya ina son ku mika min gaisuwata ga Senata Ahmad Sani Yarima, Allah Ya kare shi a kan makiya. Amin. Daga Nasiru Sani Gusau. 07064340375.

Ta’aziyyar Fatima Hassan
Assalamu alaikum Aminiya, don Allah ki mika mini ta’aziyya ta zuwa ga iyaye da mijin marigayiya Fatima Hassan Mahmud Allah ya jikanta ya saka mata da aljanna Firdausi; makasa kuwa su ji tsoron Allah, su daina. Daga Tumsiya Muhammad Bidda. 07030634428.

Ga Kwamishinan ayyuka na Kano
Salam. Jaridarmu mai farin jini ku mika jinjinata ga Kwamishinan Ayyuka na Kano, Alhaji Abba K. Yusuf, sakamakon kula da bibiyar aikin da ake  ba dare, ba rana. Yanzu Kano ta dauki harami haske ko’ina. Daga Muftahu Bala Sheshe da Ibrahim I.G.I Ma’ajin Falasdinawa, Kano 08053567865.

Ga Gwamna Murtala Nyako
Aminiya ki ba ni dama in roki Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako, da ya yara mana hanyar Yolde-Pate, bayan Sabon Tasha da damuna tabo yana kayar da mu, ijn an yi ruwan sama ba mai fita aiki. Da rani kuma kura in kana da asuma to ka rika zuwa asibiti ken an, har ranin ya kare. Daga Ishaku Ibrahim Yolde-Pate Yola 08034959465.

Albishir ga Kanawa
Salam. Amintacciyya don Allah ku taya ni yi wa al’ummar garin masoya Annabi albishir, da cewa kakarsu tan a daf da yanke saka. Domin muna nan muna ta roko da rarrashi da ban baki ga Alhaji Siddik Aminu dantata da ya taimaka mu zabe shi Gwamna, ko Allah Ya dawo mana da zaman lafiya da hada-hadar kasuwanci. Daga Zakariyya Zakariyya 08058599037.

Murna ga Safiya Musa
Safiya Musa ina yi miki murna. Allah Ya ba ku zaman lafiya, Allah Ya ba ku Abin da mai zuma ba ya so. Daga Mai kaunarki Shitu Adamu Agala 08022280149.

Ga sauyi Katsinawa
Aminiya gidn albarka, jaridar talaka. Allah Ya kareku. Ina bai wa Katsinawa shawara da su zabi Abdul’Aziz Musa ’Yar’aduwa a matsayin Gwamna a shekarar 2015. Domin na yi mafarki har sua biyu, APC ta kafa gwamnati, sauyi ya zo. Daga naku Aminu N. Kano 08056096552.

Ga Murtala Nyako
Assalamu alaikum. Gwamna Murtala Nyako, an rike mana sakamakon jarabawa saboda ka hana kudin jarrabawa. Daga Isiyaku Matawalle Yola. 08034959465

Talaka ba mutum ba
Mu dai jama’ar Najeriya mun zama saniyar tatsa, kowa da ya tashi sai ya ce talaka. Wai shi talaka ba mutum ba ne? Daga Dini Kala Kazaure 08068659591.

Gaisuwa ga FKD
Salam. Aminiya gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga babban kamfanin FKD da kuma babban darakta, Malam Aminu Saira. Daga 08068122836.

Janar Muhammadu Buhari, muna kara jinjina maka kan hakurinka. Don haka ka kara hakuri. Allah yana tare da masu hakuri. Daga Sani Abdu Beta 07068223015.

Ga jaridar Dailytrust
Dailytrust ki ci gaba da fadin gaskiya a Arewa. Daga Jibrin Garo Maileda Area 2, Abuja.

Aminiya ni ba Bakano ba ne
Assalamu alaikum idan na yi laifi ne, na tuba a rika bugo sakona; in kuma don na fito daga Sakkwato ne, ba zan ce ni Bakano ba ne. Daga Murtala Jinjiri Wamako 08123435900.

Ga Gwamna Yero
Assalam. Edita don Allah a nema mana mafita, don ma’aikatan masarautar Zazzau babu ci gaba a aikinsu, kuma ba a biyan fansho da garatuti, ga wadanda suka bari, ko suka mutu. Don Allah Gwamnan Kaduna kasa a bincika wannan matsala. A taimaka. Don akwai masu neman hakkinsu, yau shekara fiye da 10, wasu 20. Daga Aminu Zariya 08057765027.

Shaye-shaye ya yi kamari a Katsina
Salam. Aminiya, shaye-shaye ya lalata ’ ya’yan mutane a Jihar Katsina. Sai ka ga yaro dan idan mutunci, amma abokai sun lalata shi da shan kayan maye. Hukumar NDLEA a yi mana agaji, a yi ta addu’a Allah Ya shirya al’ummarmu baki daya. Amin. Daga Fatima Isyaku kofar Durbi 08141925685.

Ga ma’aikatan Aminiya
Salamun alaikum. Zuwa ga ma’aikatan Aminiya, na turo muku da sako fiye da 15, amma ni mai ban taba gani kun sa mini sakona ba. Allah Ya yi mana canji mai amfani a Najeriya. Ku huta lafiya. Daga Ado M. Garba Kibiya. 08051534212.