A duk lokacin da al’umma ke hangen matsala ta kaura a Najeriya, to a daidai wannan lokacin wata matsalar za ta fito fili, wanda har ya sa ake yi wa kasar lakabi da ‘rigar sarka kin fi karfin yaro.’ Ga dai matsalar fansho nan ta yi wa ma’aikata da dama illa, ta yadda sai an jni jiki za a ci gajiyar dan abin da aka taralokacin d amutum ke yin aikin.
A shekarun baya akwai wata matsalar da ke ci wa mahukuntan Najeriya tuwo a kwarya, wato ita ce; mafi yawa daga cikin ma’aikatan gwamnati na shiga mawuyacin hali lokaci kadan bayan ajiye aiki, wanda hakan ya yi sanadiyyar idan ka ga tsohon ma’aikaci sai ka rantse da Allah bai taba yin aikin Gwamnati ba, saboda halin da ya shiga. A yunkurin gwamnatin wancan lokacin ta Cif Olusegun Obasanjo na magance wannan matsalar ta kirkiro da wani sabon tsari ga ma’aikata, musamman na karkashin ikon gwamnatin tarayya, wanda tsarin ya tanadi wani asusun ajiya na musamman (Account) ga kowane ma’aikaci, wato asusun fansho (IBTC pension), wanda zai samu kudin shiga daga albashin ma’aikatan, tare da taimakon gwamnatin tarayya.
Hakika wannan tsarin mai kyau ne a zahirance, amma a aikace abu ne mai wahalar gaske a aiwatar da shi yadda ya kamata, kuma abin tambaya a nan shi ne; mene ne fa’idar abin? Shin wannan tsarin ya magance matsalar da ta sa aka kirkire shi? Su kansu wadanda aka yi tsarin domin su, sun gamsu da tsarin?
Idan muka dauki bangaren ma’aikatan da ake cire wa wani kaso daga cikin albashinsu da sunan Adashen Gata za mu ga mafi yawa daga cikinsu na kyamar wannan tsarin, kuma suna daukarsa da wukar nesa ce, wadda ba ta maganin mussan. Saboda duk mawuyacin halin da za ka shiga ba za ka iya amfana da ko Naira daya ba. Kuma suna zargin wasu mutane kalilan ne, tare da bankuna da ke ajiyar kudin ke amfana da su, amma ba masu su ba. Haka zalika idan ma’aikaci ya kammala aiki ko ya rasu yana cikin aiki, to ba karamin jidali ba ne idan yana bukatar kudinsa, ko magada na son hakkinsu, to za su ba ka tausayi, domin wasu magadan sai dai su yi Allah ya isa. Domin ka’idojin za a gindaya musu an tabbatar ba za su iya cika su ba.
Sannan akwai tsari makamancin wannan da gwamnatin ta wancan lokacin Cif Olusegun Obasanjo ta kawo, wanda ya tanadi duk wani karamin ma’aikaci da ke manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya, masinjoji da masu gadi da masu shara a maida su a karkashin ikon kamfanoni. Hakika wannan tsarin ma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, saboda akwai tarin matsalolin da suka yi wa tsarin katutu. daya daga ciki, shi ne, ma’aikaci ba shi garatuti balle fansho. Sai dai irin wancan tsarin da na fada a baya na asusun fansho. Duk da tarin matsalolin da ke tattare da shi. Wata matsalar ita ce yadda mutum daya ne a zaune wuri daya yana ci da gumin al’umma.
A karshe zan yi amfani da wannan damar in yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari, musamman a sanin da na yi masa na kyamar duk wani abin da yake na zalunci, to ya waiwaya a wannan bangaren domin wadanda ke cikinsa na cikin halin rashin tabbas a aikinsu.
Allah Ya sa wannan kiran ya kai inda ya dace amin.
Daga: Adamu Aliyu Amo, Katsina. Sakataren kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina. 09097300909
[email protected].
Ko asusun fansho na da amfani ga ma’aikaci?
A duk lokacin da al’umma ke hangen matsala ta kaura a Najeriya, to a daidai wannan lokacin wata matsalar za ta fito fili, wanda har…