✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko akwai sauyi a kwanaki 100 gwamnonin Najeriya?

Tabbas ‘yan magana kan ce ‘bikin Magajiya ba ya hana na Magaji,’ domin kuwa ana ta fadar albarkacin baki game da kwanakin Gwamnatin tarayya 100…

Tabbas ‘yan magana kan ce ‘bikin Magajiya ba ya hana na Magaji,’ domin kuwa ana ta fadar albarkacin baki game da kwanakin Gwamnatin tarayya 100 a karagar mulki. To ko ya abin yake ga Gwamnatocinmu na jihohi? Ko shakka babu wasu sun taka rawa, wasu kam sai dai ma a ce sun kasa gano bakin zaren kama makamar aikin. Yalwata wa al’ummominsu da alkawuran da suka sha alwashin yi wa talakawan a lokutan da suke yakin neman zaben zama a karagar mulkin.
Uwa uba yadda wasu suka fara da ruguje gidajen talakwan su da hana sana’o’i ba bisa ka’ida ba, da soke abin da yake ba wajibi ba, daga abin da suka gada a tsohon hannu.
Wasu kam shiru kake ji sai shegen yawo zuwa ketare daga dimbin ayyuka a jahohinsu sun yi wurgi da su. Ga ambaliyar ruwa ta rutsa da jama’ar su, in ban da jaje, babu jajen baka da suka yi, uwa-uba sun hana Ilimi ya habaka sai kurin fada a baka, babu cikawa. Wasu kuwa makudan kudi suka ware don gina wa kansu gidan shiga, sun manta ba shi ne abin farawa ba. Domin Wanda ya sha bama-bamai da jarraba iri-iri ya kamata a ginawa gida da farko; tare da daukar  ’ya’yansu don kula da su, sun sa kafa, sun take kansu suka sani. Anya wadannan su ne shugabannin  da suka dace da mu?
A nawa ra’ayin babu wata rawa da wasu GWAMNONIN NAJERIYA suka taka a kwana darin nan (100). Hakkinsu ne mu talakawan mu fito mu kalubalence su.  Domin ko shakka babu su ne zabinmu, wadanda kowa ya sani mun samu sahihin zabe a kasar mu ba ko ko kwanto. Su muka zaba ashe kuwa yanzu ya zama dole su bi umarnin mu, ba shawara ba. Maganar shawara ta kare sai dai umarni da abin da al’ummarka suke bukata wanda ka yi alkawari a baya, da ma wanda ya cancanta, ko kuma mu bi hanyoyin dawo da wanda ya saba ka’ida.
Hafizu Balarabe Gusau, Shugaban Muryar Talaka na Jihar Zamfara 07035304499