✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko a soja akwai tausayi

A makon da ya wuce rundunar sojojin Najeriya ta yanke wa sojoji 12 hukuncin kisa, ta hanyar harbewa, bayan da kotun soja ta same su…

A makon da ya wuce rundunar sojojin Najeriya ta yanke wa sojoji 12 hukuncin kisa, ta hanyar harbewa, bayan da kotun soja ta same su da laifin tawaye. Wadanda aka yanke wa hukuncin, suna cikin mutum 18 da aka tuhuma da laifukan rashin biyayya da yunkurin kisa./an kuma yanke wa soja guda hukuncin daurin shekara 28, tare da aiki mai tsanani, sannan aka wanke wasu mutum biyar.
An ruwaito cewa, wadanda aka yanke wa hukuncin sun harbi motar kwamandansu, Manjo-Janar Ahmadu Mohammed, wanda ya shugabanci runduna ta bakwai, a ranar 14 ga watan Mayun 2014, a Maiduguri. A lokacin da al’amarin ya auku, sojojin sun harzuka ne bayan da suka ji cewa, ’yan Boko Haram sun yi wa ’yan uwansu kwanton bauna, sun kashe su, don haka suka huce haushi a kan shugabanninsu. Rahotanni sun nuna cewa, sojoji na da tabbacin cewa, ’yan kunar bakin waken na da makaman da suka fi nasu, shi ya sa suka ki bin umarnin komawa wuraren aikinsu cikin dare.
An dai tuhumi sojojin da yunkurin kashe Janar Muhammad. Mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa, an kuma yanke musu hukuncin kisan ne, saboda laifin kulla makirci da yunkurin kisa. Mutanen sun hada da Kofural Jasper Braidolor da Kofural Dabid Musa da Lansi Kofural Friday Onun da Lansi Kofural Yusuf Shu’aibu da Lansi Kofural Igomu Emmanuel da Firabet Andrew Ngbede. Sauran su ne Firabet Nurudeen Ahmad da Firabet Ifeanyi Alukhagbe da Firabet Alao Samuel da Firabet Amadi Chukwudi da Firabet Allan Linus da Lansi Kofural Stephen Clement. Laifuka shida da aka tuhume su, su ne: (1)Laifin kulla makircin rashin biyayya (2) tawaye (3) yunkurin kisa (4) kin bin umarni (5) dabi’ar rashin biyayya (6) zargin karya. Firabet Ichoho Jeremiah, an ba shi daurin wata guda, saboda barin wurin aiki ba tare da izini ba. Wadanda aka wanke su daga tuhumar, su ne Kofural Dabid Luhbit da Kofural Muhammad Sani da Firabet Ubong da Firabet Gwaba da Firabet Inama Samuel.
Da yake yanke hukuncin, Shugaban Kotun, Birgediya-Janar C.C. Okonkwo, ya yi nuni da cewa hukuncin kotun al’amari da ya dogara kan tabbaci. Al’adar soja ta tanadi a gudanar da bincike kan dalilan da suka hifar da tawaye. Babban Hafsan Sojan Najeriya, Laftanar Janar Kenneth Minimah, a wajen wani taro da aka gudanar a Enugu, ya tabbatar da cewa hukuncin ‘laifin tawaye kisa ne.’ Wannan sako a bayyane yake:sojojin na sane da wannan matsanancin hukunci kan abin da suka aikata, tun sa’adda suka kama aiki a kashin kansu.
Tawaye da rashin biyayya wajen cin mutuncin Janar, al’amarin ya kai makura wajen rashin girmama hukuma. Rashin biyayya ga hukuma shi ne mafi munin laifi da ke nuni da rashin da’a a aikin soja. Wannan al’amari da ya auku, ya share fagen muhawara kan yadda za a rika daukar sojoji, saboda akwai bukatar a bibiyi hanyoyi da ake bi a halin yanzu, inda ke yin watsi da bibiyar tarihin mai neman shiga aikin soja, har ta kai ga manyan masu aikata miyagun laifuka na smaun shiga. Horo da yawan horar da sojoji, musmaman kananan kurata, kan yadda za su gabatar korafinsu, zai taimaka wajen gyara dabi’un sojojin da suka baude.
Duk da cewa haka al’amarin ya kasance, akwai bukatar hukumomin soja su yi la’akari da abin da ya harzuka sojojin har suka kai ga fandarewa. Ba da dadewa ba, aka zargi hukumomin soja da rike kudin da aka ware don sayen makamai tasre da biyan hakkokin kyautata rayuwar sojoji. An dade da sanin jarumtar sojojin Najeriya a wannan yanki da ma nahiyar baki daya, wajen tabbatar da zaman lafiya. Sai dai abin takaicin game da sojojin, yadda ’yan kunar bakin waken ke shammatarsu, da samun makamai wadanda suka fi na su, a wadannan ’yan shekaru, alama’arin da ya sanya ake ta bijiro da tambayoyi kan alakar shugabannin soja da cusa siyasa.
kungiyar Lauyoyin Najeriya ta NBA da ta kwadago TUC, da sauran daidaikun mutane da kungiyoyi, sun roki a yi wa sojoji 12 da ak yanke wa hukuncin kisa afuwa. Shugaban kungiyar Lauyoyi ta NBA, Augistine Alegeh ya yi nuni da cewa, tuni kasar nan ta yi rashin sojoji da dama a lokacin da tashe-tashen hankulan ’yan kunar bakin wake. Ba tare da yin watsi da hakkin hukumomin soja ba, wajen dabbaka dokokin da ke juya akalar jami’ansu, mun shiga gungun masu rokon afuwa game da wannan matsanancin hukunci da aka yanke.