✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiwon salwa na da matukar riba – Masana

Wani mai gidan gona a Minna babban birnin Jihar Neja, mai suna Mista Mathew Nuhu, ya ce kiwon tsunsun salwa na daya daga cikin wadannda…

Wani mai gidan gona a Minna babban birnin Jihar Neja, mai suna Mista Mathew Nuhu, ya ce kiwon tsunsun salwa na daya daga cikin wadannda suka fi kowane kiwo riba.

Nuhu ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) haka ne a Minna inda ya ce, kiwon salwa na da matukar riba sanadiyyar amfanin namanta da kwanta.

Ya ce, salwa tana da kuzari haka idan dan Adam ya ci namanta zai kara masa kuzari yayin da kwanta yake gina jiki da taimakawa wajen magance cututtuka.

“Kwan Salwa ya fi amfani a jikin dan Adam fiye da na sauran tsuntsaye. An fi saninsa da abincin da ke samar wa jama’a lafiya musamman masu cututtukan da suka hada da: Asma da gyambon ciki (Olsa) da hawan jinim” inji shi.

Makiyayin ya ce, ana saurin samun riba fiye da sauran halittun  da ake kiwo, saboda yawan bukatun naman Salwa da kwanta.

Nuhu ya ce, sakamakon ribar da kasuwancin kiwon Salwa ke kawowa, don haka aka samun babbar kasuwar da kawai ta masu kiwon salwa ce yau a Najeriya.

Nuhu ya kara da cewa, da jari kadan mutum zai iya samun fegin da zai yi kiwon, kuma kiwon yana da saukin gudanarwa saboda karancin ma’aikata da za su lura da kiwon. Don haka duk wanda ya shiga harkar kiwon salwa a cikin lokacin kankane zai samu riba mai yawa.

Nuhu ya ce,  ya fara da ’yan tsaki 500 da kudinsu ya kai Naira dubu 70 da kejin katako biyu da kudinsu ya kai Naira dubu 30 kowanne a gidansa da ke Minna. “Lokacin da tsuntsayen suka fara yin kwai bayan mako shida za a iya samun kwayaye 400 a duk rana, ya danganta da irin yadda ake ciyar da su abinci. Ina sayar da kiret din kwai mai guda 30 a kan Naira dubu 1,” inji shi.

Ya ce, tsuntsayen za su ci gaba da yin kwai ne har zuwa lokacin da aka ci gaba da ba su abinci, kamar kaji ba wadanda suke yin kwai kuma suna ci gaba da tsufa karfinsu na raguwa.

Nuhu ya ce, yana ciyar da tsuntsayen sau uku a rana, yayin da kayan zuba musu abinci sai ya kasance cikin tsabta don kauce wa aukuwar cututtuka.

Nuhu mai shekara 53 ya karanci harkar noma  a Jami’ar  Usman Danfodiyo (UDU) da ke Sakkwato.