✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kishirwa’ ya kashe mutum 20 a saharar Libya

Ana tunanin sun mutu ne tun kwana 14 da suka wuce

Ma’aikatan ceto sun tsinto gawarwakin wasu ‘yan ci-rani su 20 a saharar Libya da ake kyautata zaton kishin ruwa ne ya yi ajalinsu.

Wani direban babbar mota ne ya tsinto gawarwakin lokacin da yake tsaka da tafiya a cikin saharar a ranar Talata, a wani waje mai nisan kilomita 320 a Kudu maso Yammacin garin Kufra da ke kan iyakar Libiya da Chadi.

Shugaban sashen da ke kula da motocin asibiti na yankin Kufra, Ibrahim Belhasan ya ce, “Direban ya yi batan-kai ne, kuma muna zargin matafiyan sun mutu ne a saharar kimanin kwana 14 da suka wuce, saboda kiran karshe da muka gani a wayar daya daga cikinsu a ranar 13 ga watan Yuni ne.”

Yankin dai wanda babu yawan mutane sosai a cikinsa na fama da tsananin zafin da ya kan haura mataki 40 a ma’aunin Celsius.

Wani bidiyo da sashen kula da motocin asibitin ya wallafa a dandalin Facebook ya nuna gawarwakin mutanen da tuni suka fara rubewa a tsakiyar sahara, a kusa da wata motar a-kori-kura.

Biyu daga cikin mutanen dai ’yan Libya ne, yayin da ragowar kuma aka yi ittifakin ’yan kasar Chadi ne da suka tsallaka Libya, inji Ibrahim Belhasan.

Hukumar Kula ’Yan Ci-rani ta Duniya dai ta kiyasta akalla ’yan ci-rani 1,500 ne suka nitse a kifewar jiragen ruwa daban-daban a tsakiyar kogin Mediterranean a bara.