Tsohuwar Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin muhimman dalilan da suka sa ta rike mukamin Ministar Kudi har sau biyu a kasar nan.
Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana haka ne a wani shirin Ingilishi na gidan rediyo BBC, mai suna ‘The Conbersation.’
Tsohuwar Ministar ta ce, mahaifinta ya koyar da ita kishin kasa, don haka ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta bayar da gudunmawar da ta dace a lokacin da take rike da mukaman gwamnati.
Dokta Ngozi Iweala ta ce, lokacin da ta rike mukamin Minista a farko, ta yi kokari wajen kawo sauye-sauye, wadanda har suka kai aka samu nasarar yafe wa Najeriya wasu basussukan da ake bin ta.
Tsohuwar Ministar ta ce, a lokacin da aka ba ta mukamin Minista na farko, ta yi fargaba, saboda rike mukamin Ministar Kudi ba karamin abu ba ne musamman a kasa kamar Najeriya.
Dokta Ngozi Iweala ta ce wa’adinta na farko a kan mukamin Minista shi ya fi ba ta wahala, amma ko da ta sake dawowa a karo na biyu, ba ta ji komai ba, saboda ta san abubuwa da dama da suke tattare da mukamin Ministar Kudin da aka sake ba ta.