Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta ce, kashe-kashen ’yan Arewa da ake yi a yankin Kudu maso Gabas, na nuni da kudirin da ’yan yankin ke da shi na fatattakar bakin kabilu mazauna yankin nasu.
Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun Shugabanta na kasa, Yerima Shettima, AYCF ta gargadi Gwamnonin yankin da lamarin ya shafa da su hanzarta daukar matakin hana kashe ’yan Arewa mazauna yankin ko kuma su fuskanci matakin shari’a.
- EFCC ta cafke Rochas Okorocha
- Kotu ta tabbatar da na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban PDP a Kano
Idan dai ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata tsagerun IPOB suka kashe wata mata tare da ’ya’yanta hudu hade da wasu mutum shida wanda baki dayansu ’yan Arewa ne mazauna Isulo, cikin Karamar Hukumar Orumba ta Arewa a Jihar Anambra.
Yayin zamanta da ta gudanar a Kaduna, AYCF ta ce kisan ’yan Arewa a yankin abin Allah-wadai ne wanda ba za ta lamunta ba.
Ta kara da cewa, tana sa ran ganin Gwamna Soludo na Jihar Anambra ya yi amfani da karfin mulkinsa wajen gaggauta daukar matakin da ya dace a kan abin da ya faru amma sai ya yi biris.
Kazalika, ta ce halin ko-in-kula da gwamnonin Kudu maso Gabas suka nuna kan lamarin duk da su ne masu wuka da nama a sha’anin tsaron Jihohinsu, tamkar nuna kudirin da suke da shi ne na yakar sauran kabilu mazauna yankunansu.
“Bisa la’akari da ’yan Arewa da aka kashe, wannan ya nuna karara cewa rayuwar mutanenmu ba ta da wata kima a Kudu maso Gabas, yankin da IPOB da ESN da sauran ’yan bindiga suke abin da suka ga dama a cikinsa.
“Shirun da Gwamnonin yankin suke yi kan hare-hare da kashe-kashen da ake yi wa ’yan uwanmu ya isa haka. Muna gargadinsu cewa, kar su dauka rauni ne ga ’yan Arewa, girmama doka da suke yi,” inji AYCF.