✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Sheikh Albani

Wadansu ’yan bindiga da suka kashe shahararen malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani a makon jiya da har yanzu jami’an tsaro ba su…

Wadansu ’yan bindiga da suka kashe shahararen malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani a makon jiya da har yanzu jami’an tsaro ba su gano su har su kama su ba abin bakin ciki da tayar da hankali ne.  A lokacin da malamin yake tuki ne ’yan bindigar suka sha gaban motarsa, ba kuma tare da bata lokaci ba suka bude wa motar wuta. Hakan ya sanya matar Albani da kuma dansa suka rasu nan take, inda aka wuce da shi asibiti daga bisani ya rasu. Almajiran malamin biyu sun samu raunika yayin harin.
Wata majiya mai tushe ta ce al’amarin ya faru ne da misalin 10:00 na dare a lokacin da Albanin yake koma wa gida a kan Titin Gaskiya da ke Zariya bayan ya kammala gudanar da wa’azi a makarantar Markazul Salafiyya da ke Tudun Wada.
An haife Sheikh Albani a Muciya ta Sabon Gari da ke Zariya. Ya karanta kwas din Information Technology a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Yola, Jihar Adamawa. Ya yi sakandaren Barewa College da ke Zariya. Kafin rasuwarsa dalibi ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda yake digiri-na-biyu a kwas din Fannin Sarrafa Wutar Lantarki. Albani shi ne shugaban makarantar Science Academy da ke Gaskiya a Zariya. Shi ne kuma shugaban cibiyar Daruth Hadith s-Salafiyyah Center a Tudun Wada, Zariya.
Ya yi fice wajen kalubalantar karantarwar kungiyar Boko Haram, wadanda suke tayar da kayar baya a Arewa maso Gabashin Najeriya. A wata hirar da ya yi da jaridar Daily Trust ya bukaci matasa su nemi ilimin boko don su tafi da zamani musamman ma yanzu da kullum ake kara samun abubuwan fasaha da kimiyya. Ya ce wannan dalili ne ya sanya ya koma jami’a don ya yi digiri na biyu.
Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kisan ko a gano dalilin yin kisan, kodayake Albani ya shahara wajen kalubalantar karantarwar kungiyar Boko Haram, domin a lokuta da dama ya rika ba tsohon shugaban kungiyar marigayi Muhammad Yusuf shawarari da hujjoji don ya janye da’awar boko haramun ne.
Albani yana da tarihin dangantaka mai tsami tsakaninsa da jami’an tsaro, ko a kwanakin baya ma an tsare shi sakamakon zargin sa da aka yi da dangantaka da kungiyar Boko Haram, hakan ya sanya ya je kotu ya kare kansa, kuma kotu ta wanke shi.
Tsakanin 1993 da 1994 wadansu mahara sun kai masa hari a wani shagon dinki a Muciya ta Sabon Gari da ke Zariya. Ya kubuta ne bayan jama’a sun kawo masa dauki. Baya ga haka an kai masa hari a gidansa sau biyu wanda kuma ba a samu nasara a kansa ba.
Dangane da kashe Albani za a iya cewa duk malamin da yake kalubalantar karantarwar kungiyar Boko Haram rayuwarsa tana cikin hadari ga garari. Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya gamu da ajalinsa a masallaci a Kano a lokacin da yake sallar Asuba, kuma shi ma ya yi fice wajen kalubalantar karantawar kungiyar Boko Haram, haka batun yake ga kisan da aka yi wa Sheikh Umar dan Mai Shiyya a Sakkwato. Abin tayar da hankali shi ne har zuwa an kasa gano wadanda suka aikata kashe-kashen ko suke da hannu wajen kashe wadannan malaman.
Al’amarin abin daure kai ne a ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kasa gano wadanda suke da hannu a cikin kashe-kashen wadannan malaman, hakan zai matukar karya alkadarin tarihin kyakkyawan aikin jami’an tsaro a kasar nan.
Muna fata kisan da aka yi wa Albani zai sanya jami’an tsaro su farka daga barcin da suke yi hade da tsage damtse wajen ganin ire-iren hakan ba su faru a gaba ba.
Ya zama dole jami’an tsaro su gano makasan da duk wani mai hannu a ciki don a yi musu hukunci mai tsanani da zai zama darasi ga duk wanda yake yunkurin aikata laifi irin wannan.