✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kisan makiyaya 2 ya fusata Gwamna El-Rufai

Gwamna El-Rufai ya yi Allah wadai da wannan daukar doka a hannu.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya fusata da kisan wasu Fulani makiyaya biyu da aka yi ranar Lahadi a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta jihar.

Tuni dai El-Rufai ya umarci jami’an tsaro su farauto wadanda suka kashe kuma suka kone matasan biyu da aka zarga da hannu a harkar satar mutane.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkoki Cikin Gidan na jihar, Samuel Aruwan ya fitar ta ce, gwamnatin za ta zauna da iyalan wadanda aka kashe saboda kara ta’azantar da su.

Rahotanni dai sun ce wasu Fulani biyu ne suka shiga Birnin Gwari sayayya, sai wasu suka fara zarginsu, wanda hakan ya sa aka kira jami’an tsaro.

Aminiya ta ruwaito yadda mutanen suka afka wa jami’an tsaron, inda suka kwace mutane biyun da ake zargi, sannan suka kashe su kuma suka kona su.

Mista Aruwan ya ce Gwamna El-Rufai ya yi Allah wadai da wannan daukar doka a hannu.

%d bloggers like this: