✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Jos: Lalong ya sa a kamo masu yada labaran karya

Gwamnan Filato ya lashi takobin hukunta masu yada sakonnin tunzura jama'a.

Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya umarci jami’an tsaro su kamo duk masu yada labaran karya ko hotuna da bidyon karya da ke iya harzuka jama’ar jihar domin a hukunta su.

Lalong ya ba da umarnin ne a lokacin wani taron gaggawan domin samun zaman lafiya da akak gudanar a gidan gwamnatin jihar bayan harin da aka kai wa matafiya Fulani aka kashe kusan 30 daga cikinsu a unguwar Gada-Biyu da ke garin Jos.

An tare Fulanin ne a kan titi a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci taron addinin Musulunci a Jihar Bauchi.

Lalong ya ce, “Ina gargadin mutanen da ke jin dadin yada sakonni da bidiyo na karya a shafukan sa da zumunta wadanda kuma za su iya tayar da zaune tsaye.

“Na umarci jami’an tsaro su tsare su, su gurfanar da su a gaban kotu domin su girbin a bin da suka shuka na tunzura jama’a da kuma yada kalaman tsana.”

Ya ja hanakli mahalarta taron gaggawar cewa an dade ana rikice-rikice a jihar kuma babu wanda hakan ya amfana.

“Saboda haka yanzu ne lokacin da za mu hada kai mu tunkari makiyan zaman lafiya da ke tsakaninmu.

“Burin gwamnatinmu ita ce tabbatar ganin mutane na zaune lafiya da juna ba tare da la’akari da kowane irin bambanci ba; Adalci shi ne abin da zai tabbatar da zaman lafiya.

“Dole mu yi aiki tukuru wajen yakar makarkashiyar ta makiyan jihar tamu da suke son fakewa da addini ko kabila su hada mu fada da juna.

“Wajibi ne mu yi fatali da wannan tsohuwar dabarar tasu da ta da hana jiharmu samun cigaba, ta kuma bata mata suna a idon duniya.

“Abin da ya kamace mu yi shi ne tallata albarkatun kasar da Allah Ya hore mana da al’adunmu da fikirorinmu mabambanta domin jawo masu zuba jari. Idan babu zaman lafiya babu wanda zai zo jiharmu ya zuwa jari,” inji Lalong.