✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Janar Alkali: Kotu ta tura mutum 19 gidan yari

Wata Babbar Kotun Jihar Filato da ke zama a garin Jos ta tura mutane 19 da ake zargi da hannun wajen bacewa da kuma kashe…

Wata Babbar Kotun Jihar Filato da ke zama a garin Jos ta tura mutane 19 da ake zargi da hannun wajen bacewa da kuma kashe tsohon Babban Jami’in Gudanarwa da Tsare-tsare na Rundunar Sojojin Najeriya, Manjo Janar Muhammad Idris Alkali (mai ritaya) gidan yari.

Kotun ta tura wadanda ake zargin gidan yari ne yayin zamanta na ranar Litinin da ta gabata.

A yayin zaman kotun an bukaci wadanda ake zargin su kare kansu bayan an tuhume su da laifin kulla makarkashiya, hadin baki da kuma laifin kashe Janar Alkali.

Babban lauyan wadanda suka shigar da kara, Emmanuel Ochoba ne, ya shigar da bayanan laifuffukan da ake tuhumar wadanda ake zargin su 19, inda magatakardar kotun ya karanta takardar a gaban alkalin kotun, Daniel Longji.

Sai dai wadanda ake zargin sun musunta aikata laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa. Daga nan lauya Ochoba ya bukaci kotu ta ci gaba da tsare wadanda ake zargin a gidan yari, sannan ya bukaci a dage sauraren karar don ya samu damar kawo shaidunsa a gaban kotu.

Alkalin kotun, Daniel Longji ya amince da hakan, inda ya dage zaman kotun, sannan ya sanya ranar 10 ga Disamba, 2018 don ci gaba da sauraren karar. Sai dai a lokacin da lauyan wadanda ake zargin, Gyang Zi yake magana da ’yan jarida bayan an dage zaman kotun, ya bayyana cewa nan take za su rubuta takardar neman belin wadanda ake zargin, kuma yana sa ran kotun za ta amince ta ba da belinsu.