Kungiyar Matasa ta Kasa, NYCN, ta yi kira ga Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, da ya gaggauta zakulo wadanda suka kashe mashawarcin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa, Ahmad Gulak, domin su fuskanci shari’a.
Matasan sun yi barazanar ayyana gwamna Uzodinma a matsayin mutumin da ba a maraba da shi a daukacin yankin Arewa.
Wata sanarwa da Mataimakin Shugaban kungiyar na kasa, Kwamred Bishop K. Douglas, ta ce, “Abin takaici ne da sosa rai a ce kashe-kashe da rashin kiyaye doka da oda na ci gaba da samun gindin zama a yankin Kudu maso Gabas.
“Dole ne gwamnatin Jihar Imo ta fito ta yi bayani kan wadanda suka kashe Gulak.
“Ci gaba da kisan ’yan Arewa tare da lalata cibiyoyin tsaro a Jihar Imo ba abu ne da za a ci gaba da lamunce masa ba,” inji shi.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya domin yi wa tufkar hanci gabanin lamarin ya rikida zuwa yakin basasa.
Mataimakin Shugaban ya kuma ce gwamnan Jihar Imo da takwarorinsa a yankin Kudu maso Gabas sun kwana da sanin cewa: “Ba za mu taba lamunce wa da ci gaba da kisan ’yan Arewar da ba su ji ba su gani ba da ma manyanmu a yankunansu; za mu fa dauki mataki.”
Kungiyar ta bai wa gwamnan Jihar Imo mako guda da ya binciki kisan gillar ko kuma ta ayyana shi a zaman makiyin Arewa wanda za a kyama ce shi a daukacin yankin.
Har wa yau, Kwamred Bishop K. Douglas ya yi kiran taron ilahirin kabilun yankin Arewa maso Gabas domin daukar kwakkwaran mataki kan gwamnan Jihar Imon idan har ba a yi adalci kan kisan gillar.