✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta rufe gidajen man fetur saboda lita ta kai N1,000

'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi.

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin ɗaukar tsauraran matakai na rufe gidajen man da ke sayar da man fetur a kan farashin da ya kai Naira 1,000 kan kowace lita.

Yawancin gidajen mai na ’yan kasuwa a yanzu, sun ƙayyade farashin man fetur a tsakanin Naira 900 zuwa Naira 1,000 kan kowace lita.

Masu waɗannan gidajen da alama ba su damu da farashin man da ake sayarwa ba a gidajen sayar da mai na Kamfanin Mai na Najeriya ke gudanarwa.

Farashin man fetur a gidajen man NNPC ya kai daga Naira 568 zuwa N617 a duk lita.

Wannan ya kan haifar da jerin gwano a gidajen man.

A yayin da ’yan Najeriya ke nuna damuwarsu kan tsadar kayan masarufi da dillalan man fetur masu zaman kansu ke yi, Gwamnatin Tarayya ta kuma sha alwashin rufe gidajen man da aka samu suna sayar da man fetur a farashi mai tsada.

Ta bayyana hakan ne ta hannun Hukumar kula da harkokin sarrafa man fetur ta Najeriya (NMDPRA)

Gwamnatin ta jaddada cewa, farashin da ’yan kasuwa ke bi a yanzu na ƙara jefa ’yan Najeriya cikin matsi. 

Sai dai ’yan kasuwa, sun yi iƙirarin cewa tun a makon da ya gabata suke sayan man fetur kan kuɗi Naira 850 kan kowace lita kuma hakan ne ya sa farashin man fetur ya yi tsada.

Sai dai mai magana da yawun NMDPRA, George Ene-Ita, ya bayar da hujjar cewa rahoton farashin man fetur da hukumar ke samu daga jami’anta a gidajen man ya sha bamban.

“Ma’aikatanmu suna ganin farashin daban ne saboda mun buƙace su da su riƙa rubuta farashin a gidajen man a kowace rana kuma ba Naira 850 suke rubutawa ba. Wakilanmu da aka tura gidajen man sun ba mu adadi na daban,” in ji shi.

Yanzu dai ana ci gaba da samun dogayen layuka a gidan mai, sakamakon ƙarancin man fetur da ake fama da shi a Najeriya.