✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kirsimeti: Shugaban Sri Lanka ya yi wa fursunoni 1,000 afuwa

Shugaban ya yi musu afuwa saboda zagayowar bikin Kirsimeti na bana.

Shugaban Kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya yi wa fursunoni sama da 1,000 afuwa tare da sakin su daga gidajen yari albarkacin bikin Kirsimeti.

Daga cikin 1,004 da aka saki a ranar Litinin akwai ’yan kasar Sri Lanka da aka daure saboda rashin biyan tara, in ji kwamishinan gidan yari Gamini Dissanayake.

Afuwar ta baya-bayan nan na zuwa ne bayan da ’yan sanda suka kama mutum kusan 15,000 a wani samame kan masu ta’amalli da miyagun kwayoyi na tsawon mako guda da ya kare a jajibirin Kirsimeti.

Sanarwar da rundunar ’yan sandan kasar ta fitar ta ce an kama mutum 13,666 da ake zargi yayin da aka tsare kusan 1,100 masu shaye-shaye kuma an tura su gidan gyaran hali.

Sri Lanka ita ce mafi yawan mabiya addinin Buddah kuma shugaban kasar a baya ya yi afuwa ga wadanda aka yanke wa hukunci a watan Mayu don bikin Vesak a kasar.