✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kirsimeti: Boko Haram sun kashe mutum 5 da yin garkuwa da wasu a Borno

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe mutum biyar sannan suka yi garkuwa da wasu mutane da dama lokacin da suka kai…

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe mutum biyar sannan suka yi garkuwa da wasu mutane da dama lokacin da suka kai wani hari a wata unguwa da ke kusa da garin Chibok a karamar Hukumar Chibok a jihar Borno.

‘Yan bangar da suke unguwar ne suka sanar da hakan, inda suka ce maharan sun shiga unguwar ne da misalin karfe 6:30 na yamma ranar Talata cikin kauyen Korogelem mai kimanin nisan kilomita 10 daga ggarin Chibok.

Rahotan ya kara da cewa, maharan sun kone gidajen jama’a da dama sannan suka yi awon gaba da kayan abinci.