Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da shirin kirkiro da sababbin masarautu a Jihar Kano da kuma amfaninsa ga talaka a jihar da sauran sassan kasar nan, inda suka bayyana ra’ayoyinsu a kan wa zai fi amfana a tsakanin talakawa da gwamnati?
Gwamnati za ta fi amfana – Maryam Sani Rogo
Daga Abbas Dalibi, Legas
Gaskiyar magana, shi talaka ko da zai amfana ba zai yi tasiri a gare shi kamar gwamnati ba, saboda kananan hukumomin da aka kirkiro masarautun ba su da ingantattun ababen more rayuwa, dadin ma shi ne kananan hukumomin da za a kirkiro wa masarautun ba lallai ne suna da asibitoci ingantattu na zamani ba balle ma’aikata kwararru, don haka da masarautun gara a ce asibitoci aka inganta, kamar a jihata ta Kano, kananan hukumomin da aka kirkiro wa sababbin masarautu idan aka duba tun daga tituna, wutar lantarki, ruwan sha, makarantu ga asibitoci duk suna bukatar gyara ko kirkiro sababbi. Don haka ina talaka ake so ya amfana da wadannan.
Gwamnati za ta fi amfana bisa ga talakawa – Hassana Ummi Umar
Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi
Ni a nawa ra’ayin kirkiro da sababbin masarautu a wasu yankunan a cikin jiha, gwamnati za ta fi talakawa cin amfaninsu, saboda idan gwamnati tana da sakonnin da za su isa da wuri a wajen talakawa za ta yi amfani da wadannan masarautu, kuma gwamnati za ta rika samun muhimman bayanai na abin da ke faruwa a masarautun, kuma matsalolin wadannan al’ummar masarautu gwamnati za ta rika sani a cikin lokaci ba tare da wata matsala ba.
Gwamnati da talakawa babu mai amfana – Abdulhameed Shehu
Daga Faruk Tahir Maigari
Lura da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a Najeriya idan aka ce an yi karin masarautu a Jihar Kano, ba karamin kashe kudi hakan zai jawo ba, domin duk masarauta akalla za ta kirkiri hakimai guda 20. Idan aka yi la’akari da kudin da za a kashe a wajen karin wadannan masarautu zai zama barnar kudi ne kawai, don haka da gwamnati da talaka duk babu mai cin riba.
Talakawane za su fi amfana – Shu’aibu Muhammad Tahir (Kuliya)
Daga Faruk Tahir Maigari
Kirkirar sababbin masarautu a Jihar Kano talakawa ne za su fi amfana, domin a yanzu kowace masarauta za ta rika amfana daga kasafin kudin jiha kai- tsaye. Maimakon tsarin baya duk an tare ayyukan ci gaba a cikin birni kawai, yanzu kuwa za a kara matso da talaka kusa da gwamnati. Don haka karin masarautu a Kano talakawa ne za su amfana.
Kirkiro masarautun siyasa ce kawai – Bello Sharada
Daga Abbas Dalibi, aLegas
A ra’ayina kirkiro da masarautu ba don ci gaban talakawa ne da amfaninsu ake ta fadi-tashin tabbatar da masarautun Gaya da Rano da Bichi da Karaye ba a jihata ta Kano ba. Wannan aikin an yi shi ne don siyasa da biyan bukatar wadansu.
In da gaske kana son raya ilimi, ka inganta lafiya, ka bunkasa harkar noma da kasuwanci da tsaro da muhalli a yankunan masarautun nan, ba sai ka raba kasashen ba da nade-naden sababbin rawuna. Tunda iko da kudi yana hannun ’yan siyasa da ma’aikata, hanyar ita ce a ba su wakilai managarta, a sakar musu mara sai su tashi daga kauye su zama maraya. Sannan a bar su da tarihinsu da al’adarsu da gadonsu na gargajiyarsu na tun fil azal.
Talakawa za su fi gwamnati amfana – Kabir Sale
Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi
Ai ko kwankwanto babu kirkiro da sababbin masarautu a cikin wasu yankuna a jiha talakkawa za su fi gwamnati amfana dari bisa dari. Kuma abin ba ya misaltuwa domin amfanin da talakawa za su ci yana da yawa. Domin talakawa za su samu kayayyakin more rayuwa daga gwamnati da kuma wasu kungiyoyi irin na kasashen Turai da manyan masu kudi na wadannan masarautu. Saboda masarautar za ta tilasta wa masu kudin su rika taimaka wa al’ummar masarautar da abubuwan more rayuwa. Don haka talakawa sun fi gwamnati amfana da kirkiro da sababbin masarautu a wasu yankunan kasar nan.