Assalamu alaikum Manyan gobe. Tare da fatan anyi Sallah lafiya kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin a kan ‘Kirkin tsuntsu’. Labarin ya yi nuni ne ga yadda yin kirki ke da matukar muhimmanci a rayuwa. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi.
Akwai wasu tsuntsaye da ke zaune a wata babbar bishiyar da ke cikin wani daji. Ba su da wurin da ya wuce saman wannan bishiya. Kuma wadannan tsuntsaye sun kasance mata da miji ne.
Ran nan sai yunwa ta dame su kuma suka rasa yadda za su yi, sai suka yanke shawarar kowa ya fita shi kadai don yawon neman abinci ko za su yi sa a.
Yamma na yi sai ita macen ta dawo sannan ta yi mamakin rashin ganin mijinta. Ta shiga sake-sake a zuciyarta can sai ta ga wani katon mutum rike da mijinta a keji.
Ta yi bakin cikin haka kuma ta rasa yadda za ta yi , ga shi kuma ana ruwan sama. Ga mutumin ya jike sosai.
Sai ta yi maza ta samo kara ta hada masa wuta ta ce da shi ya ji dumi ganin ya jike sharkaf sannan ta kara da cewa idan ya gama za ta fata cikin wutar don ta gasu, daga nan sai ya samu naman da zai ci..
Wannan kirkin da ta yi wa wannan mutumin ya sa tausayinta ya kama shi kuma ya sakar mata mijinta daga keji.