Rejoice Afebli wadda yanzu ta koma Dunu Rejoice Zainab, ta haddace Alkur’ani bayan ta Musulunta, kuma yanzu haka take sanya nikabi.
Ga tattaunawa Aminiya da Zainab wadda dalibar ajin karshe ne da ke karantar Ilimin Hada Magunguna a Jami’a.
Mene ne tarihinki a takaice?
Mahaifina dan kasar Ghana ne kuma Kirista mai suna Mista Michael Afebli, amma mahaifiyata Misis Otaru Aina Florence wadda ita ma Kirista ce ’yar garin Ogaminana da ke Jihar Kogi ce.
Mahaifina yana da makaranta, amma yanzu an sayar da makarantar, mahaifiyata ta rasu ina da shekara 12, amma tun ina da shekara 9 rabon da in gan ta. Na yi firamare a Makarantar Board of Glory Primary School, sannan na yi qaramar sakandare a Covenant Junior High School.
Na kammala a Anlo Senior High School a 2015, sannan na fara karatu a Jami’ar Cape Coast, tsakanin 2015 zuwa 2017duka a qasar Ghana kafin in dawo Najeriya, inda na fara karantar Ilimin Haxa Magunguna a Jami’ar Ilori daga 2017 zuwa yanzu.
Ina jin harshen Ewe da Twin na kasar Ghana, sai Yarbanci da Inglishi.
Lokacin da nake sakandare a Ghana, na kasance mai bin addinin Kiristanci sau-da-kafa, domin har wa’azi ina fita saboda ina da yakinin duk abin da kake yi, yana da kyau ka yi shi da kyau, har ta kai na fara tunanin kaiwa lokacin da zan daina zunubi baki daya.
Yaya aka yi kika zama Musulma?
Duk da cewa a cikin danginmu na nesa akwai Musulmi, iyayena dukkansu Kiristoci ne na gidi.
Bayan na kammala sakandare, sai na zo Najeriya inda na fara zama a shagon sayar da maganin wata maqwabciyarmu kafin in fara jami’a.
Ashe akwai shirin da Allah Yake yi min wanda ya fi wannan, domin ta sanadiyarta ne na zama Musulma.
Ina son matar sosai da iyalinta musamman yanayin shigarsu da halayyarsu. Sai na fara tunanin wai mene ne a cikin addininsu da ya sa suke rayuwa haka.
Cikin ikon Allah sai na Musulunta kafin in fara karatun jami’a a Ghana. Alhamdulillahi.
Wane kalubale kika fuskanta daga iyaye da ’yan uwa da abokai?
Iyayena sun ba ni goyon baya sosai. Watakila da mahaifiyata tana raye da ba za ta amince a cikin sauki ba. Mahaifina mutum ne wayayye mai ilimi. Har sai da ta kai wasu abokansa suna yi masa magana cewa yaya zai bari in zama Mmusulma
Lokacin ne ya kira ni yana fada, sai na fada masa cewa ya duba a tsakanin ni da sauran ’ya’yansa da ’ya’yan abokansa wa ya fi halaye masu kyau da kokarin karatu da sauransu, sai ya dubi maganata.
Tun daga lokacin bai sake yi min maganar ba. Bayan wannan ban fuskanci wani kalubale ba gaskiya.
Kin taba fuskantar kalubale daga wasu masu bukatar cewa lallai dole ki koma Kirista?
Na sha fama da irin wannan, amma da yake lokacin da nake Kirista da gaske na rike addinin, sai ya kasance ayoyin da suke kawo min na fi su sanin su da fahimtar su, yanzu ne kawai na fara manta ayoyin.
Sai da na fara fahimtar Musulunci na fahimci bambancin. Amma a lokuta da dama idan muna irin wannan muhawarar, idan na ga sun fara sakin layi, sai in bar maganar.
Yaushe kika haddace Alkur’ani Mai Girma?
Bayan na Musulunta ne na fara karatu a Jami’ar Cape Coast da ke Ghana.
Sai na fara zama da wasu Musulmi mata guda biyu masu sanya nikabi; daya ta haddace Qur’ani, dayar kuma ta haddace rabi.
Wannan ne ya ba ni sha’awa, sannan na fara sha’awar shiga irin tasu duk da cewa lokacin ba ni da ilimin addini sosai.
Amma da yake duk abin da nake yi da gaske nake yi, sai na fara sanya nikabi. Cikin ikon Allah tu ina Ghana na haddace daga Mujadala zuwa Nasi.
Kuma wani abin mamaki na yi haddar ce ba tare da sanin bakaken Larabci ba. Kawai na yi haddar ce ta hanyar sauraro.
Na sha wahala, amma ina godiya ga Allah domin wannan ne ya taimaka min wajen samun sasauƙin karasa haddar.
Bayan na dawo Najeriya, sai na faro daga farko wajen wani malami da na fara karatu a wajensa na Larabci da Kur’ani.
Yanzu na haddace Kur’ani a makarantar Assunnah Academy of Arabic and Islamic Studies da ke Tanke a Ilọrin na Jihar Kwara.
Wane babban kalubale kika fuskanta a wajen haddar?
Akwai kalubale da dama. Dole na dawo baya da aji daya a karatun jami’a domin mayar da hankali wajen haddar Qur’ani.
Amma duk da haka na samu nasara a aji dayan, duk da cewa ba yadda ya kamata ba, saboda da a ce bokon kawai na yi, da zan fi cin jarrabawar, amma ina sane da hakan, na dan rage lokacin karatun bokon domin haddar Kur’ani.
Kuma kasancewar ina karatun Hada Magunguna ne, shi ma yana bukatar lokaci sosai, wanda hakan ya sa hada guda biyun ya ba ni wahala sosai.
Haka samun malamar Kur’ani shi ma ya ba ni tangarda domin na fi son malama mace, amma da zarar mun fara sai mu zama kawaye, sai karatun ya fara kasa.
Wannan ya sa na yi malaman Qur’ani da yawa. Akwai wadanda muka fara karatun da su, amma sun kasa ci gaba.
Hakan ya shafi karatuna, amma alhamdulillahi ban yi asara ba kuma na samu saukin wasu abubuwa watakia saboda Allah Ya ga zuciyata.
Mene ne burinki a gaba?
Babban burina shi ne koyar da ’ya’yana a gida ta yadda idan an tambaye su wa ya koyar da su addini, za su fada cikin alfahari cewa wajen mahaifiyarsu.
Wannan yana cikin burina a duniya kuma hakan ya taimaka min wajen kara kaimi. Sannan nakan ziyarci wasu kawayena a lokacin hutu, inda nake jin dadin yadda suke tilawar Kur’ani.
Shin kin fuskanci matsalar rashin kudi a lokacin karatunki?
Ban fuskanci matsalar kudi ba, ina godiya ga Allah. Ba ni da mahaifiya, sannan mahaifina yakan yi rashin lafiya ya shiga rashin kudi, amma Allah Yana taimako na ta hanyar wasu. Ba su taba bari na fuskanci rashi ba.
Me kike shirin yi nan da wasu shekaru?
In sha Allah a matsayina na ’ya mace mai neman ilimi, zan so in koya kira’o’i. Yanzu kira’a daya kawai na iya, zan so in koyi sauran 9 din.
Sannan zan yi aure in sha Allah, in samu ’ya’ya sannan in ci gaba da karatu har matakin digirin digirgir domin in taimaki al’umma.
Akwai wani abu da kike da-na-sani?
Babu ko kadan. ’Yan uwana Kiristoci ne masu ilimi da wayewa, duk lokacin da na je hutu a Ghana wanda har yanzu ina zuwa, idan lokacin Sallar Asuba ya yi, su ne suke tashi na daga barci. Haka suke tuna min duk idan lokacin Sallah ya yi.
Wata kawata ce take son in sa sunan Zainab da na Musulunta, sannan aka ce min sunan daya daga cikin ’ya’yan Manzon Allah (SAW) ne.
Mene ne sakonki na karshe?
Ba zan ce na yi abubuwa cikin sauki ba, amma Allah Ya saukaka min komai, wannan ya sa akwai amfani mutum ya kasance yana da buri mai kyau a rayuwa.
Burin kasancewa cikin mafi soyuwa a wajen Allah wato ma’abota Alkur’ani, wannan kadai abin nema ne. Mata su ne iyayen gida, don haka zai fi kyau su dage wajen neman ilimin addini.