Masallacin Salihiyya, Wadi Addawasir, Saudiyya
Fassarar Salihu Makera
Huduba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya halitta mu domin mu bauta maSa mu kadaita Shi, kuma Ya yi mana baiwa da girmawa ta yi maSa tasbihi da tahamidi. Ina gode maSa Matsarkaki, kuma ina gode maSa, Ya yi wa masu gode maSa alkawarin kari. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida lallai Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, mafi girman ManzanninSa kuma mafi daukakar bayinSa. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ku bi Allah da takawa, ku girmama Shi, ku ji tsoronSa, ku kiyaye Shi. Ku sani lallai Shi- Mai girman Daraja – Ya siffantu da siffofin daukaka da kamala da girma da fiffiko. Ya daukaka kuma Ya tsarkaka daga abokan tarayya da abokin kwatantawa da misaltawa.
Ya ku Musulmi! A tare da mu a cikin wannan huduba wani Hadisi ne mai girma, wanda ya kunshi wani tari na ilimi guda goma. Abu Idris Khaulani (Allah Ya yi masa rahama) daya daga cikin maruwaitansa, idan zai karanta shi yakan gurfana a kan gwiwoyinsa, domin girmamawa da martabawa gare shi.
Hadisin shi ne:
“An karbo daga Abu Zarrin (RA) daga Annabi (SAW) cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa Mai girma da daukaka cewa lallai Shi Ya ce:
“Ya ku bayiNa! Lallai ne Ni na haramta zalunci a kaiNa, kuma Na sanya shi abin haramtawa a tsakaninku, don haka kada ku yi zalunci.
Ya ku bayiNa! Dukanku batattu ne, sai wanda Na shiryar da shi, don haka ku nemi shiryarwaTa, in shiryar da ku.
Ya ku bayiNa! Dukanku mayunwata ne, sai wanda Na ciyar da shi, don haka ku nemi ciyarwaTa, in ciyar da ku.
Ya ku bayiNa! Dukanku huntaye ne, sai wanda Na tufatar da shi, don haka ku nemi tufatarwaTa, in tufatar da ku.
Ya ku bayiNa! Lallai ku kuna kuskure dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai baki daya, don haka ku nemi gafaraTa, in gafarta muku.
Ya ku bayiNa! Ba za ku iya cutar da Ni ba, balle ku cutar da Ni, kuma ba za ku iya amfanar da Ni ba, balle ku amfanar da Ni.
Ya ku bayiNa! Da dai na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan (irin) zuciyar mafi takawar cikinku, wannan ba zai kara komai a cikin mulkiNa ba.
Ya ku bayiNa! Da dai na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan (irin) zuciyar mafi fajircin mutum daga cikinku, wannan ba zai rage komai daga cikin mulkiNa ba.
Ya ku bayiNa! Da dai na farkonku da mutanenku da aljanunku za su taru a fili guda kuma su roke Ni, in ba kowane mutum abin da ya roka, hakan ba zai rage komai daga cikin abin da Nake da shi ba, sai kamar yadda allura za ta iya rage wani abu in aka jefa ta a teku!
Ya ku bayiNa! Abin sani kawai ayyukanku ne Nake lissafa muku, sa’annan in sakanka muku a kansu. Don haka wanda ya samu alheri sai ya gode wa Allah. Wanda ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa sai kansa.” (Muslim ne ya ruwaito shi).
Ya ku Musulmi! Wannan Hadisin kudisi da Manzonmu Mai daraja ya ruwaito mana daga Ubangijinmu Mai girma, hakika ya kunshi kiraye-kiraye goma da Ubangijinmu Tabaraka Wa Ta’ala ya yi, Yana mai ilimantar da mu da shiryar da mu da kwadaitar da mu.
Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku bayiNa! Lallai ne Ni na haramta zalunci a kaiNa, kuma Na sanya shi abin haramtawa a tsakaninku, don haka kada ku yi zalunci.”
Wannan shi ne kira na farko, inda a cikinsa Allah Madaukaki Yake bayyana tsarkakarSa daga yin zalunci domin cikar adalcinSa da sonSa ga adala da ayyukan falala. Sannan Ya haramta mana yin zalunci a tsakanimu, ba ya halatta ga wani ya zalunci wani.
Ya ku muminai! Lallai zalunci duffai ne a Ranar kiyama. Zalunci kuma shi ne tauye hakkin wadansu da yi musu ta’addanci. Kuma babban abin bakin ciki ana samun haka a tsakanin al’umma. Gidaje nawa ne ake samu zalunci a tsakanin ma’aurata? Kuma iyaye nawa ne suke gaza sauke hakkin da ke kansu game da ’ya’ya maza da mata? Maza nawa ne suke kwace dukiyar matansu in sun kasance ma’aikata ko suna kasuwancin ko sana’a? Wani ma yana ganin wannan hakkinsa ne. wannan haramun ne kuma zalunci ne. Idan ba ta yarda ko ta yafe masa ba, Ranar kiyama zai biya ta da kyawawan ayyukansa!
Da yawa ba ana zaluntar mata wajen rabon gado ba, sai maza su cinye su bar mata (misali abin da ya shafi gadon gonaki musamman mutanen karkara)?
Kuma nawa ne zalunci yake gudana a tsakanin makwabta? Ko kuwa mai karfi nawa ne ke taushe mai rauni? Kuma zalunci nawa ne ake samu daga ma’aikatan da aka danka amanar marasa galihu a hannunsu, inda za su rika zaluntarsu ta hanyoyi daban-daban da dabara iri-iri, su cinye hakkokinsu, su dauki abin da bai halatta ba su hana su wani da sauransu. Kuma idan marar galihun ya nemi hakkinsa babu mai sauraronsa, ta yiwu wannan ya shafi hanyar tura shi makaranta ce a wani wuri ko abinci ne da bai san da shi ba. To ga Allah muke mika kukan wadannan raunana!
Ya ku Musulmi! Amma kiraye-kiraye na biyu da na uku da na hudu su ne fadin Mai girma da daukaka a cikin wannan Hadisi na kudisi cewa: “Ya ku bayiNa! Dukanku batattu ne, sai wanda Na shiryar da shi, don haka ku nemi shiryarwaTa, in shiryar da ku. Ya ku bayiNa! Dukanku mayunwata ne, sai wanda Na ciyar da shi, don haka ku nemi ciyarwaTa, in ciyar da ku. Ya ku bayiNa! Dukanku huntaye ne, sai wanda Na tufatar da shi, don haka ku nemi tufatarwaTa, in tufatar da ku.”
Allahu Akbar! Ku dubi wadannan kyawawan kalmomi daga Ubangiji Mai shiryarwa Mai jinkai. Lallai shiryarwa tana hannunSa amma mu batattu ne sai in Ya shiryar da mu. Karkatattu ne sai in Ya nuna mana hanya Ya kama hannunwanmu zuwa ga daidai. Kuma domin cimma haka ne Ya aiko mana da ManzonSa Annabi Muhammad (SAW) saboda ya nuna mana hanyar, kuma Ya saukar mana da Alkur’ani domin mu karanta shi mu rika binsa.
Lallai mu mayuwanta ne sai idan Allah Ya ciyar da mu daga arzikinSa. Huntaye marasa sutura sai in Allah Ya suturta mu da suturarSa. Don haka muke da bukatuwa zuwa ga suturcewarSa da sutura ta zahiri kuma muke bukatar suturarSa -Madaukaki- sutura ta ma’anawi, ita ce takawa. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku ’ya’yan Adam! Lallai ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tana rufe muku al’aurarku, kuma da kawa (ado). Kuma tufar takawa waccan ce mafi alheri. Waccan daga ayoyin Allah ne, tsammaninsu suna tunawa.” (k:7:26).
Amma kira na shida ku saurare shi: “Ya ku bayiNa! Lallai ne ku kuna aikata laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gaba daya, don haka ku nemi gafaraTa, in gafarta muku.”
Na’am, lallai ne mu masu bijirowa ne ga zunubai da karkacewa, don haka wajibi ne a kanmu mu rika gaggawar tuba da gyara abubuwan da muka bata. Don haka ya ku muminai ku guji tabbatuwa a kan aikata zunubi. Ku sani kowane dan Adam mai kuskure ne mai aikata zunubi ne, amma mafiya alherin masu kuskure ko aikata zunubi su ne masu yawan tuba.
Ku ciru daga aikata zunubi kuna masu ikhlasi ga Allah wajen yi haka, masu azama a kan ba za su koma ga aikata zunubi ba, idan kuma kun yi zunubin ne wajen tauye hakkin ’ya’yan Adam to ku nemi yafiyarsu tare mayar musu abin da kuka zalunce su.
Ya ku Musulmi! Amma kira na bakwai daga Ubangiji Mai girma shi ne fadinSa: “Ya ku bayiNa! Lallai ne ku ba za ku iya kawai ga cutar da Ni ba, balle ku cutar da Ni, kuma ba za ku iya kaiwa ga amfanar da Ni ba, balle ku amfanar da Ni.”
Haka ne, lallai ne Ubangjinmu Madaukaki Shi ne Mahalicci, shi ba abin halitta ba ne. Shi ne Ubangiji, waninSa ne marbubi, Shi Wadatacce ne, waninSa fakiri mai rauni. Da mutane da aljanu da mala’iku za su taru a kan su motsa misalin kwayar zarra a duniya, ba za su iya ba, sai da umarninSa da izininSa, to ta yaya za su iya kaiwa ga cutar da Allah Madaukaki?
Amma jumla ta bakwai da ta takwas su ne fadinSa Mai tsarki: “Ya ku bayiNa! Da dai na farkonku da na karshenku, mutanenku da aljanunku za su zamo da irin zuciyar mafi takawar cikinku, wannan ba zai kara komai a cikin mulkiNa ba. Kuma ya ku bayiNa! Da dai na farkonku da na karshenku, mutanenku da aljanunku za su zamo da irin zuciyar mafi fajircin cikinku, wannan ba zai rage komai daga cikin mulkiNa ba!”
Ya ku Musulmi! Lallai ne Allah -Mai girman Daraja – da’ar masu da’a ba ta amfanarSa, kuma sabon masu sabo ba ta cutar da Shi. Abin sani wanda yake amfana da ayyukan da’a ko ya cutu da ayyukan sabo, shi ne mukallafi daga cikin mutane da aljanu. da’a raha ce da natsuwa a duniya kuma ita ce sababi ta shigarka Aljanna. Sabo kuma shu’umci ne da bakin ciki da nadama a duniya kuma hanya ce ta shiga wuta a Ranar kiyama in dai ba ka gaggauta tuba zuwa ga Mai gafara Mai jinkai ba.
Wadanne kiraye-kiraye ne suka fi wadannan kiraye-kiraye kyau? Ku dubi wadannan maganganu masu kyau. Ina fadin abin da kuke ji, ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku, kuma ku nemi gafararSa, lallai ne Shi (Allah) Mai gafara ne Mai jinkai.