Matukar al’umma za su kasance ’yan tsaki da tunani irin na dila da dabi’ar zaki a dawa, to wannan al’umma ta kara lalacewa za ta rika yi. Rayuwa irin ta dan tsako komai ya samu shi kadai ne ba ta dace ba. A yau ba ma kishin kasarmu, mutum kawai matansa da ’ya’yansa kawai yake yi wa hidima bai damu da al’umma ba. Dabi’ar dila kuma shi ne wayo. A yau tunaninmu yaya za samu ko da wani zai rasa. Dabi’ar zaki da muka dauka ita ce danniya da nuna isa a kan na kasa. A yau kowa ya samu dama sai ka ga zaluncinsa ya bayyana a fili. Gaba daya sai ka rasa wane ne mai gaskiya a cikinmu. Idan har muna so kasarmu ta ci gaba, ta zama abar koyi dole sai mun dauki kishin kasarmu, mun sa a zukatanmu, mun kuma cire kabilanci na yanki, harshe, addini a dukan lamuranmu.
Daga Nasiru Kainuwa Hadeja 08100229688/09073801967