✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kira ga talakawan Najeriya kan zaben Nagari

Salam, fatan alheri a gare ku ma’aikatan jaridar Aminiya. Edita ka ba ni dama in yi kira ga ’yan uwana talakawan Najeriya, zabe yana kara…

Salam, fatan alheri a gare ku ma’aikatan jaridar Aminiya. Edita ka ba ni dama in yi kira ga ’yan uwana talakawan Najeriya, zabe yana kara karatowa, yana da kyau talakawa.mu natsu wajen zaben shugabanni nagari, masu kaunarmu da kishinmu, ba masu neman tara abin duniya ba. Mu lura da kyau wajen zaben nagari a kowace jam’iyya yake, ba lallai sai mutum yana wata jam’iyya mai gwamnati shi ne yake tsarkakakke ba. A kowace jam’iyya mutum yake muddin mun san ya cancanta mu zabe shi, a kau da batun jam’iyya a zabi cancanta shi ne alheri. Allah Ya taimaki Najeriya, Allah Ya azurta Najeriya da tarin masu kaunarmu, amin.

Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki Kano, 07068295953.