Ci gaba daga makon jiya
Idan muka dubi yadda mutane suke amfani da lokutansu a wannan zamanin, “Abin babu sakainar diba”. Musamman mata, wandanda su ya fi kamata su kiyaye lokutansu matuka saboda rawar da suke takawa a wajen gyaran al’umma. Wasu matan da zarar gari ya waye, suka tura yara makaranta, sai su rungumi wannan waya ta zamani wadda kusan komai yana ciki, sai su yi ta yin ‘games’ ko kallon fina-finai na shirme wadanda ba za su amfane su ba duniya da lahira .Sannan uwa uba tana hada mutum da mutum a duk inda yake a fadin duniyar nan. Wannan ne ya sa za ka ga wata macen idan ta dukufa tana yin hira da mutanenta a waya ta hanyar ‘Whats App’ ko ‘Face Book’ da sauransu, to ta manta da duk sauran harkokin da za su amfane ta da iyalinta da ma sauran al’umma.
Mata sukan manta da abubuwa masu muhimmanci, domin hatta lokacin sallah sai ya wuce ba ta san ya wuce ba. Wadda aka yi sa a kuma ta iya tashi ta yi sallar, Allah- Allah take ta idar ta ci gaba da taba waya. Babu zancen natsuwa a cikin sallar. Aiyukan gida kuwa babu lokacinsu, haka za ta bar gidanta kaca-kaca, babu shara , babu wanke-wanke, tana fama da waya. Zancen kula da yara kuwa , bayan sun dawo daga makaranta, babu shi, sai dai kowa ya fita ya yi harkarsa.Sai ta ji kukan wani yaron, wata kila sannan ta nemi shi. Babu zancen duba littattafan yara , balle a koya musu aiyukan da ba su iya ba.
Wannan waya ta sa wasu matan kullum sai dai su dafa wa ‘ya’yansu taliyar indomie, hatta maigida idan ya dawo sai dai nan da nan a dafa masa indomie, to babu lokacin da za a yi wa iyali girki mai dadi, koda maigida ya kawo kayan cefane, Whats App da kallon fina-finai sun cinye lokacin .Kuma wani abin takaicin ma shi ne hatta lokacin da za a ware a dafa indomie ta yi dadi babu, domin kuwa da wayar ake shiga kicin din, ana dafa indomie ana taba waya, da haka har abinci ya kone, haka za a ci babu dadi.
Wannan bata lokaci da mata suke yi a shirme abu ne wanda bai dace ba. Domin wasu matan hatta maigidansu ba su da lokacinsa matukar suna yin Whats App ko Facebook da sauraunsu. Domin akwai mijin da ya saki matarsa sakamakon kin amsa wayarsa saboda tana Whats App da mutanenta. Kuma ya rubuto mata sako, amma ta ki ba shi amsa, domin ba ta da lokacinsa. Kuma da ma ya gaji da halinta domin ba ta kula da gida kwata- kwata, hatta yaronta karami ba ta iya kula da shi, saboda haka kawai ya sake ta .Ya ce ta je ta yi Whats App sosai da kawayenta.
Idan mata yawanci duk suka mayar da hankalinsu ga waya, to wace irin gudunmuwa za su bayar wajen gyaran alumma? Kuma ba za su iya hana ‘ya’yansu ba,tun da su ma ’ya’yan suna ganin abin da iyayensu suke yi. Ba za su samu lokacin da za su yi tunanin abubuwa masu muhimmanci domin kawo ci gaban alumma ba. Saboda haka abubuwa sai su yi ta ci gaba da rikicewa.
Ba a ce mata kada su yi amfani da waya ba, ai Hausawa ma suna cewa:“Taba kida , taba karatu”.Amma komai da lokacinsa. Domin kuwa idan kika yi kyakkyawan amfani da waya, za ki karu da ita sosai. Haka nan idan kika yi amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba, za ki yi nadama duniya da lahira. Domin kuwa kullum lokaci tafiya yake yi, kwanakin karewa suke yi, tunaninki kullum yana kan waya, kin manta da addininki, kin manta da iyalinki, kin manta da ‘yan uwanki. Sannan kin manta cewa ke mai kiwo ce,kuma Allah Zai tambaye ki game da kiwon da Ya ba ki.
Ya kamata mata ku sani cewa waya tana da muhimmanci kuma tana da illoli. Don haka kamata ya yi ku tsara lokacinku yadda ya dace, Kada ku bari waya ta rika yi muku yakin sunkuru. Ku san yadda za ku rika amfani da wayoyinku yadda ya kamata. Kada ku bari waya ta rude ku, ku manta da kawunanku. Kuma ku sani cewa shi lokaci ba ya jira. Kuma duk wanda ya bata lokaci, haka shi ma lokacin zai bata shi. Saboda haka sai a yi hattara. Allah Ya ganar da mu.