✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Keshi ya fitar da sunayen ’yan kwallon da za su tafi gasar cin kofin duniya

A ranar Talatar da ta wuce ne Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya fitar da sunayen ‘yan kwallon da yake tunanin…

A ranar Talatar da ta wuce ne Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya fitar da sunayen ‘yan kwallon da yake tunanin zai tafi da su gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a wata mai zuwa.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Premium Times ta kalato, ta ce kocin ya bayyana sunayen ’yan kwallo 30 ne inda daga ciki yake shirin zaftare 7 su koma 23 wadanda zai tafi da su gasar cin kofin duniya.
Sai dai kocin ya cire sunayen Ikechukwu Uche da kumaBrown Ideye da hakan ta jawo korafi daga wasu daga cikin masana harkar kwallo.
Daga cikin ’yan kwallon da Kocin ya gayyata akwai bincent Enyeama da Austin Ejide da Chigozie Agbin da Daniel Akpeyi.  Sannan ya kira Elderson Echeijile da Juwon Oshaniwa da Efe Ambrose da Godfrey Oboabona da Azubuike Egwuekwe da Kenneth Omeruo da Joseph Yobo da Kunle Udunlami.
Sauran sun hada da John Mikel Obi da Ogenyi Onazi da Ramon Azeez da Ejike Uzeonyi da Sunday Mba da Gabriel Rueben da Nosa Igiebor da Joel Obi da Micheal Uchebo.  Sannan akwai ’yan wasan gaba irin su Ahmed Musa da Shola Ameobi da bictor Moses da Emmanuel Emenike da bictor Nsofor da Osaze Odemwingie da Micheal Babatunde da Nmandi Odumadi da kuma Nwofor Uche.
Ana sa ran ’yan kwallon  za su hadu a sansanin horar da su ne a ranar 26 ga Mayun nan a Abuja kafin daga bisani a zabi 23 daga ciki wadanda za su tafi gasar cin kofin duniya a Brazil a wata mai zuwa.