✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kenya ta kori Lauya Miguna kan ‘rantsar’ da Odinga

kasar Kenya ta kori wani dan adawa kuma lauya mai suna Miguna Miguna, sakamakon rawar da ya taka wajen rantsar da jagoran ’yan adawa Raila…

kasar Kenya ta kori wani dan adawa kuma lauya mai suna Miguna Miguna, sakamakon rawar da ya taka wajen rantsar da jagoran ’yan adawa Raila Odinga a matsayin “Shugaban kasar Talakawa.”

Mista Miguna ya bar kasar Kenya a jirgin sama zuwa kasar Kanada, inda yake da takardar zama dan kasar.

Gwamnatin Kenya ta zargi Mista Miguna da sarayar da matsayinsa na dan kasar Kenya, zargin da ya musanta.

 In za a iya tunawa a daidai lokacin kaddamar da Odinga, gwamnatin Kenya ta dode daukacin gidajen talabijin din kasar ta yadda ba za su iya watsa bikin ba.  

Mista Odinga dai ya kaurace wa zaben da aka sake a karshen bara, inda ya ce an shirya magudi don samun nasarar Shugaba Uhuru Kenyatta.

Shi da magoya bayansa suna daukar kansa a matsayin halattaccen Shugaban Kenya.

A watan Agustan bara ne Mista Odinga ya fafata da Shugaba Kenyatta inda ya sha kasa, amma rKotun kolin kasar ta ce an yi magudi a zaben inda aka sake zabe a watan Oktoba.

Sai dai Odinga ya ki shiga zaben na biyu, inda Kenyatta ya lashe zaben da kashi 98 cikin 100 a zaben da kashi 30 cikin 100 na masu kada kuri’a suka yi zabe.

Bayan wata biyu da kama ragamar mulki da Kenyatta ya yi ne sai Odinga ya ratsar da kansa Shugaban kasa a Dandalin Uhuru da ke Nairobi a ranar 30 ga Janairun bana.

Mista  Miguna Miguna shi ne jagoran wata kungiyar turjiya mai suna National Resistance Mobement (NRM),  wadda take dasawa da jam’iyyun adawa.

Kuma a ranar 30 ga Janairu gwamnatin Kenya ta ayyana kungiyar da kungiyar masu aikata miyagun laifuffuka.

 Ba wannan ne karo na farko da Miguna yake sa kafar wando daya da mahukunta ba. A 1988 gwamnatin Daniel Arap Moi ta lokacin ta kama shi. Daga baya Miguna ya tafi kasar Kanada inda ya yi da’awar shi fursunan siyasa ne kamar yadda shafinsa na Intanet ya tabbatar.

A shekarar 2017 ne ya fara goyon bayan Odinga, alhali shekara biyar baya ya rubuta wani littafi mai suna Peeling Back the Mask, inda a ciki ya yi kaca-kaca da salon mulkin Odinga a matsayinsa na Firayi Ministan Kenya. 

A shekarar 2013 dai ya goyi bayan Shugaba Kenyatta ne a zaben Shugaban kasa.