Hukumar kula da shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta amince kasar Kenya ta dauki nauyin gasar cin kofin Afirka na ’yan gida da aka fi sani da Championship of African Nations (CHAN) a shekarar 2018.
Kenya ta zamo ta biyu da ta fito daga yankin Gabashin Afirka wacce za ta dauki nauyin gasar. Sannan Ruwanda wacce ta fito daga yankin Tsakiyar Afirka ce za ta dauki nauyin gasar a shekarar 2016 a sanarwar da Hukumar CAF ta yi a karshen makon jiya.
kasar Libya ce ta lashe gasar da aka kammala a watan jiya a Afirka ta Kudu bayan ta lallasa ta Ghana a bugun fanariti a wasan karshe.
Dimokuradiyyar Kongo ce ta lashe ta 2009 yayin da Tunisiya kuma ta lashe ta 2013.
Ita dai wannan gasa an kirkiro ta ne don ba ’yan kwallon da ke wasa a kasashensu ba tare da sun fita kasashen ketare ba damar nuna bajintarsu. Hakan na taimakawa wajen zakulo zaratan ’yan kwallon da ke wasa a kasashensu na asali.
Da yawa daga cikin ’yan kwallon Najeriya da suka halarci gasar a Afirka ta Kudu sun samu nasarar ketarewa zuwa wasu kasashe don cigaba da yin kwallo.
Kenya ce za ta dauki nauyin gasar cin kofin Afirka na ’yan gida (CHAN) a shekarar 2018
Hukumar kula da shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta amince kasar Kenya ta dauki nauyin gasar cin kofin Afirka na ’yan gida da aka…
