✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Keken watsattsake!

A rana ta sili ga watan Noman-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje na shiga kurkurido tare da abokan kwadagona,…

A rana ta sili ga watan Noman-Baba na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje na shiga kurkurido tare da abokan kwadagona, inda muka yi wa Haurubja tsinke tun daga birnin Dabo inda ba a dabo. Mun kusa kutsa kai cikin wannan babban birni na kasar Haurobiya, sai kawai muka yi kicibis da wani mai dan kulki ya yi kikam a titi, yana yi mana walwalin waliyo da cocila, don haka mai jan linzamin kurkuridonmu ya ja ya tsaya cak. Shi kuwa wannan jami’I sai ya yi bijiro mana da tambayoyi, tun daga kan lasisi zuwa sauran takardun izinin jan kurkurido, mu kuwa sai ba shi amsa muke yi.

daukacin fasinjojin kurkuridon mu duk a Kamfanin Dalilin-taron-su suke laluben kadago a wajen kwadago, in ban da Yaron Malam mai jan linzami. Da mai taku da dan kulki ya Ankara cewa, wannan kurkuridon na dauke da tambarin Kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya, sai kawai ya daina yi mana tambayoyi, ya yi tsuwwa, ya ce,” Keken watsattsake!”
Wannan lamari na mai dan taku da kulki, dakon giwa hula bugu da kari ya haifar mana da ce ce – ku ce, inda kowa ke bayyana abin da ya fasko, har ta kai ga an lakaba mana sunan “keken watsattsdake,” kuma an sallame mu nan take, ba tare da wani bata lokaci ba. Kai mai jan linzami ma har bayyana yadda suka yi wata takaddama da mai kulki a birnin Dabo; shi ma ya yi sa’a, domin da isar su ofishin masu dakon giwa sai Babban Oga ya bayar da umarnin a sake shi, amma ta cikin harshensu na masu kulki. Kai in takaice maka zance, masu taku da kulki suna bijiro da batutuwa a cuccure, tamkar masu yren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba. “Da babban Oga ya ce a yi ciki da ni, sai na ji mai sajen tkau da kulki ya roki Oga kan lallai ya sa a yi masa ca’ammasa, wato ya samu abin motsa mukamiki tamkar a birnin Tagadas,” a cewar mai jan linzamin kurkurido.
Ni dai ina kujerara bayan kurkurido, ban ce komai ba game da wannan ;lamari na mai dan taklu da kulki. Dominj na fasko cewa ba su dade da dain karbar abin tauna marsa ba, tun da a zamanin mulkin mulaka’u na jam’iyya maiu dan boto da sanda jirge, babu abin da zai hana ku yi ciniki da su kafin su bar ka ka wuce. Hasalima mu masu balaguro a titunan Haurubja, muka dauka cewa wannan sun bude shago ne; an baje haja ana ta hada-hada. Ni dai babu ruwana.
Haurobiyawa, abin da nike son nusar da mu game da labarin mai dauke da tambarin giwa yana taku da dan kulki, shi ne wannan gwamnati da ke jan ragamar al’umma tana fafutikar hana kwashi-kwaraf da dukiyar kasa, wadda a da wasu suka fantama, suka yi wadakar son ransu da ita. Kuma ko na karbar goriyar marsa a tsakanin jami’an tsorata al’umma, ni dai ban cika bijiro da kamuya-muyar da suke yi ba. Domin tun tuni na ji ana cewa laifi dai tudu ne, wato take naka ka hango na wani.
Sai dai wani hanzari ba shekawa a cikin sana’ar durwa ba, mu kamfanin buga amintattun jaridun Haurobiya yana ta kokarin kange mu daga kamuya-miya, kai hasalima cewa aka yi, idan an dan jinka maka ‘’yan matsabbai sai kawai ka ce, ‘a’a, a bari,’ ko kuma idan ka kanga gilashi, ka murguda baki kamar kana cin kilishi, sai ka furta cewa, “Nonon tanklin yuyu.” Don haka ni ke da tabbacin cewa, wanda duk aka jinka masa matsabbai ko ya karbi marsa a gogoriyon goriya daushe, to a harshen Ingilishi ya yi “yasar tankin yuyu.”
Haurobiyawa a rage camma da cacumar marsa, amma idan an je birnin Tagadas sai a motsa mukamuki wajen cin ca’ammas. Kuma mutum ya iya dan make maka d amalku, don gudun kada ’yar Jihar Zaman-fara ta yi gusun da shi a wajen Gusau. Lallai mu rika bin ka’ida don mu samu fa’ida. Mu bi dokja don kada a yi mana duka.
Batu na ingarman karfen karafa, a duk lokacin da ‘yan rahoton mujallu dsa akwatunanm Magana suka smau labarin mutum ya aikata alheri ko sharri, tabbas za su baza wa duniya ta ji, amma ba manufarmu ba ce mu yi wa wani tonon sili, tamkar yadda shafin tonon sililin wirkilili ya yi wa Amurkawa.
Sannan akwai dimnin masu watsattsake da buda wagagen littattafai da suka samu martaba a cikin da wajen kasar Haurobiya. Kai hasali ma bayan mun rabu da mai dakon giwa yana taku da dan kulki, na binciki shafukan mashakatar lilo da tsallake-tsallake, ind ana yi kicibis da labarin yadda mutanen Mao Zedong suka karrama wani marubuci a birnin Bajintar Sinawa. Kuma wannan marubuci ya yi bajintar bayyana yadda masu fardar gayauna ke samar da dimbin kayan dundume kururu a fadin duniya. Ni ma da na ji labarin da na kasa furta sunan wannan gwanin watsatttsake sai kawai na lakaba masa Jan-dawo. Ga dai yadda labarinsa yake:
“Kasuwar masu fade gayauna a birnin Bajintar Sinawa ta gayyaci wani kwararren mai watsattsake da buda wagagen litattafai dan kasar Jamus, mai suna “Jan Douwe ban der Ploeg,” don tattaunawa da shi game da dan kitabinsa mai taken: Takun talakawan zamani a sana’ar na-duke: Fafutikar ’yanci mai dorewa a farfajiyar dunkulalliyar duniya. Masu hada-hadar kasuwanci kayan dundume kururu da ake samarwa a sana’ar na-duke da limbu-limbu a cikin lambu da fade gayauna, wani gagarumin gwanin mai watsattsake ya bayyana cewa, takun kanannan masu farde gayauna na iya samar da tulin kayan dundume kururu da kumbura tumbi; ga bunkasar harkar neman kadago a wajen kwadago. Sannan an tabbatar da cewa masu fardar gayauna, su tada kwarin kunya, sun kunyata ’yar Jihar Zaman-fara, domin ’yar Gusau babu yadda za a yi ta yayime su zuwa gusun da gari..”
’Yan makaranta zan karkare batutuwana, ta hanyar nusar da mu irin bukatar da ake da ita wajen ganin kowane saurayi ya shiga cikin rukukin farde gayauna, idan kuma gargjejen kato ne, to da rani mu ganshi ya yi limbu-limbu a cikin lambu. Domin sanin kowa ne man tunkuza ya zakuda da baya a wajen bunkasa tattalin arziki. Saboda haka nike nusar da mu muhimmanci da ke tattare da zama Hauren-Hatsi, musamman jin cewa, masu yaren hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, na cewa, ‘hantsi ba hatsi hadari.” Kuma da ruwan tumbi a ke jan na kwakware.
Ian fatan mai dakon giwar tsare dokokin Haurobiya ya fasko irin watsattsaken da muke a kamfanion buga amintattun jaridun kasar Haurobiya. Kuma ni tukin tsaye ma nike yi a wajen watsattsake da buda wagagen littattafai. Sannan idan na ziyarci kauyenmu wta sa’ da nike ake farde gayauna. Lallai mu daina kwashi-kwaraf ko laluben goriyar marsa. Ni dai ba ruwana idan aka cinno wa mutum, Loma-a-murde, duk das hi ma ana neman a mnurde shi tunda ya zama muzurun Lami.