✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kebin-Prince Boateng ya koma FC Barcelona

A ranar Talatar da ta gabata ce kulob din FC Barcelona ya bayar da sanarwar daukar Kebin-Prince Boateng a matsayin dan kwallonsa. Kulob din, kamar yadda…

A ranar Talatar da ta gabata ce kulob din FC Barcelona ya bayar da sanarwar daukar Kebin-Prince Boateng a matsayin dan kwallonsa.

Kulob din, kamar yadda ya sanar a shafin sadarwarsa ya ce ya sayo Boateng ne daga kulob din Sassuolo na Italiya a matsayin aro.

Boateng mai kimanin shekara 31, dan asalin Ghana yana cikin ’yan kwallon da suka wakilci Ghana a gasar cin Kofin Duniya a shekarar 2006.

Barcelona ta ce ta sayi dan kwallon ne don maye gurbin dan kwallonta Munir El-Haddadi da ta sayar ga kulob din Sebilla a makon jiya.

Boateng ya buga wa kulob din Sassuolo wasanni sau 13 a bana, inda ya samu nasarar jefa kwallo hudu a raga.

Boateng ya canja sheka zuwa kulob din Sassuolo na Italiya ne daga kulob din Eintracht Frankfurt na Jamus a bara kuma ya samu nasarar lashe Kofin DFB-Pokal bayan sun lallasa kulob din Bayern Munich da ci 2-0 a wasan karshe.