Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan kayan hadin soyayyar ma’aurata. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
4. Kyakykyawar niyyar zaman aure: Wannan shi ne sinadari na hudu a kayan hadin da ke gina kyakykyawar soyayya a tsakanin ma’aurata. Kyakykyawar niyyar zaman aure ita ce ya kasance tun farko ma’aurata sun kulla kyakykyawar niyyar yin kwakwkwaran riko ga igiyar aurensu; ya kasance tun fil’azal sun yi kudirin komai zai faru, ba za su bari aurensu ya mutu ba. Wato ya kasance ma’aurata na muradin ci gaban rayuwar aurensu komai runtsi komai tsanani. Wannan sinadari shi ne mafi alfanu ga dadewar rayuwar aure a tsakanin ma’aurata, domin ko babu sauran sinadaran nan uku da bayaninsu ya gabata, wannan kadai yana iya tallabar aure har ya yi tsawon rai na ban mamaki. In ma’aurata suka kudiri aniya, kuma suka sa a ransu cewa za su kasance ma’auratan juna na har abada, komai wuya komai dadi, to wannan zai sa su yin tsananin taka-tsantsan wajen kiyaye duk wani abu da zai kawo cikas a rayuwar aurensu kuma zai sa su yi nisan hakuri da juna a mafi yawan al’amura.
In ma’aurata suka sa muradin kasancewa tare har abada sama da komai a matsayin burinsu, to za su yi komai na ganin cewa aurensu ya ginu sosai kuma ya kafu sosai; za su dage komai wahala su rike igiyar aurensu ba za su yi sakaci da ita ba.
Aure ibada ne kamar sauran ibadu, don haka babban abin da ke sa aure ya yi albarka shi ne in ya kasance tun farko an kyautata niyyar cewa za a yi ne don Allah kadai da fatar samun lada daga gare Shi ba don wata manufa ba, yin haka samun karin karfin gwiwa ne wajen daure duk wasu matsaloli, wahalhalu da jarrabawar da ka iya tasowa a rayuwar aure. Kamar yadda komai wuya komai dadi, duk Musulmin kirki zai yi riko ga ibadarsa kamar Sallah da Azumi, to haka ma komai wuyar zaman aure sai a daure a rike gam, wannan shi zai sa a dace duniya da Lahira.
Amma abin takaici shi ne irin wannan kyakyawar niyya ta yi karanci a irin aurarrakin wannan zamani, kwata-kwata ba a bin dokokin addini wajen neman auren, kulla auren da kuma wajen zaman aure, wannan ya haifar da yawaitar mutuwar aure a wannan zamani. Da yawan ma’aurata ba don kwadayin bautar Allah suke yin auren ba, suna yi ne don kwadayin wasu bukatun duniya.
Raunin wannan sinadari a zuciyar ma’aurata shi ke kawo yawan mutuwar aure, tun farko in ma’aurata sun yi niyyar yin aure na har abada, to ko me zai faru za su ci gaba da riko ga igiyar aurensu. Aure ana yin sa ne har abada ba don a yi a rabu ba, amma da yawan ma’aurata suna aure ne da wata manufa ta daban a zuciyarsu wacce ba ita ce ta mutu-ka-raba ba. Wannan shi ke sa matsaloli su yi ta tasowa a zaman aurensu har ya kai su ga rabuwa.
Muradun da ke sa ma’aurata yin riko ga aure
Ingantaccen muradi: Shi ne muradin son kasancewa tare don Allah kadai da niyyar kyautata ibada ba don wata bukatar duniya mai karewa ba; shi ne ma’aurata su ba rayuwar auratayyarsu muhimmanci sama da komai; ta haka ne za su iya sadaukarwa domin ganin ta ginu, ta kafu kuma ta dore har abada.
Ingantaccen muradi ya kasu biyu: Akwai masu yin kyakykyawan riko ga aurensu saboda Allah da girmama ibadar auren da suke yi, kuma suna yin haka ne cikin dadin rai ba a kan dole ba, wato ba wata bukatar da ta sanya su dole su yi haka din. Akwai kuma masu riko ga aurensu saboda Allah amma a kan dole, misali ma’auratan da ya kasance sun samu baraka a aurensu, amma suna zaune tare zaman hakuri saboda Allah ba don wata bukatarsu ba, ko kuma irin wadanda iyaye suka tilasta su zaman auren da ba sa so, suka daure don yin biyayya ga iyayensu; maigida ko uwargidan da ake muzgunamawa cikin rayuwar aure amma suka daure suna zaman hakuri ko zaman ’ya’ya saboda Allah.
Muradi na dole: Shi ne in ya kasance ma’aurata na muradin kasancewa tare kawai don wata bukata tasu wadda in babu ita ba za su yi wannan muradin ba. Kamar wadanda suke tare kawai don ’ya’ya, ko don tsoron abin da rabuwarsu za ta haifar cikin danginsu; ko don tsoron surutun mutane; wadansu matan na zaune da mazansu ne kawai saboda abin hannunsu ko matsayinsu; wadansu kuma mazan suna zaune da matan da ba su jin dadin zama da su amma ba su iya rabuwa da su saboda kyawunsu ko asalinsu.
Muradi na bogi: Shi ne in ya kasance ma’aurata na muradin kasancewa tare ne kawai lokacin da suke cikin jin dadi da juna, amma da wata ’yar matsala ta taso, ba tunanin da zai fado musu sai na rabuwa da juna. Dan abin da bai kai ya kawo ba sai ya sa uwargida na fadin na gaji da wannan aure! Ko maigida ya ce mene ne amfanin zama da ke? Da ire-iren wadannan. Ma’auratan da suke da irin wannan muradi na bogi, da wuya aurensu ya kai labari.
Rashin muradi: Haka kuma akan samu ma’auratan da komai ya ji a rayuwar aurensu, ga soyayya, abota, ga kuma fahimtar juna, amma saboda ba su ba auren nasu muhimmanci sama da sauran abubuwan rayuwarsu ba, hakan na iya sa aurensu ya kasa tsawon rai; misali: kamar mijin da zai ce dole sai matarsa ta bar aiki ko wani abu makamancin haka: in ta ki bari har hakan ya kai ga mutuwar auren, wannan ya nuna su duka ba su muradin auren ke nan, ita ta ba aikin da take yi muhimmanci sama da aurenta, shi ma mijin ya kasa sadaukar da bukatarsa don dorewar rayuwar aurensu.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.