✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kauyen da mutanensa ke fama da ciwon mantuwa

Akasarin masu cutar sun haura shekara 60 sai wasu 10 da suke kasa da haka.

Kauyen Landais Alzheimer da ke Kudu maso Yammacin Faransa, kauye ne da ke da bambanci da sauran kauyuka musamman a Turai.

Domin duk mutanen da ke cikin kauyen masu fama wata larura ko kuma ciwo ne na mantuwa da ake kira Alheimers.

Kauyen ba irin kayukanmu da na sauran wuraren jama’a ba ne da za ka ga ana hadahadar cinikayya ko aiki ko fadi-tashin rayuwa da sana’o’i da irie-irensu ba, a kauyen ba a komai sai kokarin gudanar da rayuwa cikin sauki da walwala kansancewar duk mazaunansa na fama da wannan cuta kuma an samar da kauyen ne don neman magani.

Ga misali, shagon da ke tsakiyar kauyen yana samar da kayan abinci masu sauki kamar su burodi mai suna Baguette amma mai shagon ba ya karbar kudi, don haka babu wanda zai tuna da cewa lalitarsa ta bata ba ko ya manta bai fito da kudi ba, in ji wani rahoton shafin BBC na Ingilishi.

Cutar mantuwa cuta ce da take damun mutane da yawa musamman wadanda suka manyanta, inda suke bukatar ganawa da likita da kuma shan magani a-kai-a-kai.

Amma maimakon a rika samun waraka sai ta dada ci-gaba, don haka aka yi tunanin sauya yadda ake tunkarar cutar ta wata hanya ta daban ba ta killace masu ita ba a asibiti ba.

A bar su su yi rayuwa irin tasu tare da yin mu’amala da juna, hakan ya sa aka samar da wannan kauye a kasar Faransa.

A inda a kauyen ya zama gida ga masu wannan cutar kimanin 120 da ma’aikata 120 da kuma masu kula da tsofaffin da masu aikin-sa-kai su ma 120.

Akasarin masu cutar sun haura shekara 60 sai wasu 10 da suke kasa da haka.

Da aka tambayi wani tsohon manomi mai suna Francis yadda ya ji a lokacin da likita ya shaida masa cewa yana da cutar mantuwa da ya koma rayuwa a kauyen, cewa ya yi, “Abin da wahala, rayuwa da cutar. Domin mahaifina ma yana da cutar mantuwar (Alzheimer)…. Ina nan (kauyen) ne don in rayu, duk da dai ba yadda aka so ba ne hakan.”

Wani tsoho mai suna Philippe ya bayyana yadda suke tafiyar da rayuwarsu a kauyen da babu wasu sa’o’i da aka kebe don alkawarurruka ko sayayya illa hira da zaman shan shayi.

“Muna fita mu dan zagaya da kafa,” in ji Philippe, yana duban nesa, inda bayan ya gama shan shayin tare da tsohuwar matarsa za su je wani wurin shakatawa, in ji rahoton.

Daya daga cikin manyan jami’an kula da kauyen mai suna Farfesa Helene Amiebe ta ce, ana sa ido sosai a kan kauyen, kuma ta ce sakamakon da ake samu na nuna cewa a zahiri zaman da tsofaffin ke yi na yin tasiri kan cutar.

Bugu da kari iyalai na samun kwanciyar hankali da sanin cewa danginsu na zaune a kauyen “Abin da muka saba gani lokacin da aka ajiye mutane a asibiti shi ne kara tabarbarewar cutarsu – abin da ba ma gani ke nan a nan.

Muna ganin yadda abubuwa suke sauyawa cikin sauki. Muna da dalilan da suke nuna cewa irin wadannan cibiyoyi na iya tasiri a kan ci-gaba a bangaren samar da magunguna,” in ji ta.