A safiyar Talata Allah Ya yi wa Kauran Katsina, Hakimin Rimi, Alhaji Nuhu Abdulkadir rasuwa.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da ta fito daga Fadar Sarkin Katsina, ta hannun Sarkin Labaran masarautar, Alhaji Ibrahim Bindawa.
- Mutum 7 sun mutu bayan ruftawar rufin masallaci a Pakistan
- Duk jami’o’i za su koma hannun gwamnatocin jihohi idan na zama Shugaban Kasa —Atiku
Tuni dai aka sallaci gawar marigayi Kauran Katsina wanda Babban Limamin Masallacin Juma’a na Katsina, Malam Dayyabu Liman ya jagoranci janazar a garin Rimi.
Gwamna Aminu Bello Masari na daga cikin wadanda suka halarci janazar tare da wasu mukarraban gwamnatin jihar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Alhaji Nuhu Abdulkadir ya bar duniya bayan shafe shekaru 80 a doron kasa.
Kazalika, marigayin wanda ya mutu ya bar ’ya’ya da jikoki ya shafe shekaru 40 a gadon sarauta, wanda yana daga cikin Majalisar Hakimai 4 masu zaben sarki a masarautar ta Katsina.
Sauran masu zaben sarkin sun hada da Galadiman Katsina, Durbin Katsina da kuma ‘Yandakan Katsina