✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kauce yaro

Wani Babarbare ne xansa ya yi masa laifi sai ya kama shi da duka, yaron ya kama gudu. Shi kuwa sai ya xauki dutse ya…

Wani Babarbare ne xansa ya yi masa laifi sai ya kama shi da duka, yaron ya kama gudu. Shi kuwa sai ya xauki dutse ya jefe shi. Da ya ga dutsen zai same shi a kai, sai ya ce: “Kauce! Yaro, kauce kada dutse ya same ka!” Yaro bai kauce ba, dutse ya same shi a kai, sai uban ya ce: “Na ce ka kauce ka qi, ga shi kanka ya fashe.”

Daga Laminu Umar Abba, 08131364647