✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsinawa uku a Legas

Wasu Katsinawa uku ne suka je Legas neman kudi. Wata rana da yamma suka ci ado suka shiga gari. Suna tafiya sai suka yi mata…

Wasu Katsinawa uku ne suka je Legas neman kudi. Wata rana da yamma suka ci ado suka shiga gari. Suna tafiya sai suka yi mata magana ta mayar musu da Turanci, su kuma ba su ji. Sai abin ya yi musu ciwo har suka kudiri aniyar koyon Turanci, ko ta halin kaka. Suka ci gaba da tafiya sai suka ga wani na waya da Turanci, sai suka matsa kusa wai za su koyi Turancin daga abin da yake fada. Ya ce, “We are three,” sai babban cikinsu ya ce ya rike wannan. Sai ya sake cewa “because of money” sai na biyu ya ce ya rike wannan. Sai mutumin nan ya ce “that is what we are waiting for,” sai na uku ya ce shi ma ya rike wannan.
Sai suka shiga gari, kowannensu na ta bitar abin da ya rike. Suna cikin tafiya sai suka ga taron jama’a sun yi da’ira a wurin wata gawa, suka kutsa kai har kusa da gawar. Can sai ga motar ’yan sanda bayan sun dan dudduba gawar, sai babban ’yan sandan ya dubi jama’ar ya ce, “Please who killed this man?” Kowa ya ki magana, kawai Bakatsine nan sai zuciyarsa ta ba shi cewa Turanci ne jama’ar ba su iya ba shi kuma ya koyo. Sai ya dan hada fuska, ya ce, “We are three.” Sai dan sandan ya ce “Because of what?” Sai daya Bakatsinen ya zaburo zai yi bajinta ya ce, “Because of money.” Sai dan sandan ya nuna Katsinawan biyu ya ce, “You are under arrest!”  Sai Bakatsine na uku ya dauka wani abin arziki ’yan uwansa suka yi, sai ya ce wa dan sandan, “That is what we are waiting for.” Shi dan sanda ya sa aka kama su.  
Daga Abdullahi Musa Hadeja 07066180429