✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katin kudi

Wani Bakauye ne ya shigo birni, yana wucewa sai ya ga mutane sun yi layi a ATM, suna ta cirar kudi, sai ya ce: “Oh,…

Wani Bakauye ne ya shigo birni, yana wucewa sai ya ga mutane sun yi layi a ATM, suna ta cirar kudi, sai ya ce: “Oh, mutanen birni da dabara, ka ga sun sa kati kawai sai su cire kudi.” Shi ma sai ya bi layi, da aka zo kansa sai ya sanya nasa katin, mashin ya rike masa kati. Wani mutum ya ce masa: Ka shiga daga cikin bankin ka fada masu. Ma’aikacin bankin ya ce: “Wane irin kati ne ka sanya?” Sai ya ce: “Wane irin kati kake tsammani, idan ba katin dan kasa ba?”
Daga Shehu Lawali Tsafe 08091573703