✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwarmu ta samu bunkasar tattalin arziki sosai – Alhaji Abdallah

Alhaji Abdallah Muhammed Caps shi ne shugaban kungiyar ’yan Kasuwar Laushi da ke Bauchi cikin tattaunawarsa da wakilinmu ya yi tsokaci game da gudunmawar da…

Alhaji Abdallah Muhammed Caps shi ne shugaban kungiyar ’yan Kasuwar Laushi da ke Bauchi cikin tattaunawarsa da wakilinmu ya yi tsokaci game da gudunmawar da ‘yan kasuwa suke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan da sauran batutuwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Farko za mu so ka fara gabatar da kanka?
Alhaji Abdallah: Sunana Alhaji Abdallah Muhammed, Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwar Laushi da ke Bauchi kuma wannan kungiya tana da tsohon tarihi kuma dukkan mambobin kungiyar ’yan kasuwa ne masu neman abin da za su ci. Akwai kungiyoyi da dama a kasar nan, amma ba su da manufofi kamar kungiyarmu. Muna da manufofi masu kyau muamman ta fuskar magance zaman kashe wando a tsakanin al’umma.
Aminiya: Yaushe kuka kafa wannan kungiyar?
Alhaji Abdallah: Mun kafa wannan kungiyar ne fiye  da shekara 15 da suka wuce. Duk bayan shekara hudu ana gudanar da zaben shugabannin kungiyar yanzu haka ni ne shugaban kungiyar na bakwai. Watannin baya da suka wuce aka rantsar da mu kuma tun lokacin da muka karbi ragamar shugabancin kungiyar babu abin da muka sa a gabanmu kamar mu ga Kasuwar Laushi ta samu ci gaba da bunkasar tattalin arziki. A gaskiya kasuwarmu ta samu bunkasar tattalin arziki sosai.
Misali a lokacin zaben Shugaban kasa da na gwamnoni wannan kungiya ta ba da gudunmawa sosai wajen shiga kafafen watsa labarai domin bayyana wa al’umma muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Babu kasar da za ta samu ci gaba a lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula.
Kafin zuwan sabuwar gwamnati, mutanen yankin Arewa maso Gabas da wasu sassan kasar nan sun fuskanci hare-hare da ’yan kunar bakin wake, amma tun lokacin da aka rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar a ranar 29 ga Mayu an fara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a masallatai da coci-coci.
Aminiya: Wane  hali ’yan kasuwar yankin Arewa maso Gabas suke ciki yanzu?
Alhaji Abdallah: Gaskiya ’yan kasuwar yankin nan sun yi fama da tashe-tashen hankula wadanda suka yi sanadiyyar gurgunta harkokin kasuwanci, saboda haka muna fata Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin shiyyar su ba da kulawa ta musamman ga ‘yan kasuwa.
 Shugaba  Buhari da gwamnoni sun cika kwanaki 100 a kan mulki tun lokacin da suka shiga ofis abubuwa suka fara sauyawa yanzu haka ana sayar da litar man fetur a kan Naira 87. ’Yan kasuwa suna daga cikin wadanda suke ba da gagarumar gudunmawa wajen magance matsalar rashin aikin yi a kowace kasa a duniya.
Aminiya: Mambobi nawa kungiyarku take da su?
Alhaji Abdallah: Yanzu haka mambobin wannan kungiya sun kai mutum dubu uku da wani abu. Kuma kowane shago akwai yara masu aiki a ciki duk shekara sai mun yaye yara a kasuwar. Kadan daga cikin manufofin kafa wannan kungiyar shi ne inganta rayuwar ’yan Kasuwar Laushi. Duk ranar Asabar muna zama domin tattauna wasu daga cikin matsalolin da muke fuskanta domin kungiya ba ta samun ci gaba sai da lissafi.
Aminiya: Wadanne matsaloli kuke fuskanta a yanzu?
Alhaji Abdallah: Kadan daga cikin matsalolin da muke fuskanta a  yanzu su ne wajen da muke ajiye motocin yana bukatar gyaran fuska duk shekara sai mun yi gyara saboda haka muna fata gwamnatin jiha za ta kawo mana dauki.
Har ila yau, yawancin mambobinmu suna fama da rashin jari a hannunsu. Kasuwanci ba ya yiwuwa yadda ya kamata, sai mutum yana da jari amma muna ci gaba da ba su hakuri duk wanda ya yi hakuri da kadan to tabbas zai samu mai yawa a gaba.