C da C wata shahararriyar kasuwa ce ta mako-mako da ke a Jihar Bauchi, wadda mata da maza ke saye da sayarwa a cikinta.
An ce, a duk ranar Juma’a mutane na zuwa kasuwar domin yin hadahadar kasuwanci daban-daban saboda kayayyaki suna da araha a can.
Kasuwar mai shekara kusan 30, ta fara ne a filin ƙwallo da ke Ƙofar Fadar Maimartaba Sarkin Bauchi, inda a lokacin ake sayar da kayan sawa na gwanjo da aka kawo daga Jos a Jihar Filato.
- Sadaukarwar ’yan Najeriya ba za ta tafi a banza ba — Tinubu
- Kasafin 2024 zai kai watan Yunin 2025 – Akpabio
Yayin da kasuwar ta samu karɓuwa, wani lokaci a baya sai hukumomin Jihar Bauchi suka mayar da ita zuwa inda take a halin yanzu, wato yankin Layin-dogo, kusa da Tashar jirgin ƙasa a unguwar Railway mai tazarar kilomita uku daga fadar sarki.
Ba kamar sauran kasuwannin jihar ba, C da C galibi mata ne suka fi zuwa sayayya, waɗanda galibinsu suka fito daga wasu ƙananan hukumomin jihar don sayan kayan sawa da kayan abinci da kayan girki da sauran kayayyaki don amfanin kansu da kuma sayar da kaya don kasuwanci.
Da yake bayyana yadda kasuwar ta fara kusan shekara 30 da suka gabata, Sakataren Ƙungiyar C da C kasuwar da ke ci ranar Jumma’a, Yakubu Muhammad Ibrahim ya ce, “a al’adance a ƙasar Hausa muna gudanar da ƙananan sana’o’i a kewayen fadar sarakuna a ranar Juma’a, domin galibi a nan ne wurin da yake zama Babban Masallacin Jumma’a.”
Ya ƙara da cewa, ‘‘don haka a al’ada, za a yi taron jama’a a kusa da irin waɗannan wuraren. Wannan kasuwa ta fara ne a matsayin wata ƙaramar cibiyar kasuwanci, amma kamar yadda kuke gani, yanzu ta faɗaɗa.”
“Kasuwar tana da albarka saboda kayayyaki, suna da araha a nan, shi ya sa mutane ke tururuwa a nan, don yin siyayya. A halin yanzu, ana iya samun duk abin da kuke so a kasuwar, tun daga kayan sawa zuwa kayan kwalliya da kayan abinci da kayan robobi da kayan kicin da sauran kayayyaki.
Yakubu Muhammad ya ƙara da cewa,“idan ka sayi kaya a kan Naira 100 a wasu kasuwannin Jihar Bauchi, idan ka zo C da C, za ka same su a kan Naira 70 ko ma Naira 60. A ɗauki shinkafa misali, idan Naira 2,000 ce a wasu kasuwanni, a nan za ka samu a kan Naira 1,700 ko Naira 1,600. A taƙaice dai, C da C kasuwa ce ga masu ƙaramin ƙarfi.”
“A halin yanzu ’yan kasuwa daga wasu jihohi suna zuwa kasuwar duk mako.
Haka kuma, kwastomomi daga lunguna da saƙo na Jihar Bauchi da sauransu suna zuwa kasuwar duk ranar Juma’a domin neman kayayyaki masu araha. Hasali ma, yawancin mutanen da suka fito daga wasu ƙananan hukumomin Jihar Bauchi ne da kuma garin Jos a Jihar Filato duk suna zuwa cin kasuwar,” In ji shi.
Al’umma sun shaida wa Aminiya cewa, yayin da kasuwar ke ci gaba da jawo hankalin abokan ciniki, ’yan kasuwa da yawa suna zuwa wurin.
An ƙiyasta cewa, aƙalla sama da mutane 8,000 ne ke yin kasuwanci a kasuwar a kowane mako.
Malama Lawiza Musa, ɗaya daga cikin masu cin kasuwar C da C ta shaida wa Aminiya cewa, ta shafe shekara 10 tana sayan kayayyaki daga kasuwar, inda ta ce kullum tana samun sauƙi a can fiye da sauran kasuwanni.
“Ina zuwa wannan kasuwa tsawon shekara 10 da suka gabata. Ina yin sana’ar sayar da kayayyakin hannu kuma koyaushe ina samun su da rahusa a wannan kasuwa. Yawancin lokaci nakan mayar da kayan zuwa ƙauye, in sayar wa masu sha’awa. Ina zuwa kasuwar kowane mako,” in ji ta.
Malam Isa Ibrahim, wani ɗan kasuwa da ke zuwa kasuwar yau da kullum da ya fito daga Jos, Jihar Filato, inda ya ce zuwa kasuwa ya zama al’ada a gare shi da sauran abokan aikinsa, inda ya ce, “nakan zo kasuwar nan ne domin sayen tufafi, domin a nan idan an kwatanta farashinsa da sauƙi a kan yadda suke a kasuwanninmu da ke Jos.
A duk ranar Juma’a, abokan aikina tsakanin 30 zuwa 60 ne ke raka ni zuwa wannan kasuwa don sayan tufafi da sauran kayayyaki. Muna samun abin da muke so a nan, saboda ’yan kasuwa daga Kano suna kawo kayayyaki iri-iri, waɗanda ake sayar da su kan farashi mai sauƙi, wanda mai ƙaramin ƙarfi zai iya samu. Shi ya sa muke zuwa nan don yin siyayya duk ranar Juma’a,” in ji shi.
Wakilin Jaridar Aminiya ya lura cewa, kasuwar ta kasu kashi-kashi, ga masu sayar da kaya da masu sayar da kayan abinci da masu sayar da robobi da kayan miya da sauransu.
Malam Abdulrahman, wani mai sana’ar sayar da kayan sawa a kasuwar shi ma ya ce, “mutane ne ke kula da kasuwar, saboda yadda ake samun kayayyaki iri-iri. Duk dillalai suna samun kaya mai rahusa a nan fiye da sauran kasuwanni. Mun gode wa Allah da yadda kasuwanci ke bunƙasa a kasuwar”.
Wani ɗan kasuwa mai suna Mustapha Kada da ke sayar da tawul da kayan sawa ya ce, “ni maɗinki ne wato tela, don haka nakan ɗinka kayayyakin mata ne da kayan da nake saya a nan gaba don in riƙa sayar wa abokan ciniki a ƙauyenmu. Haka kuma, ina samun riba daga wannan ƙaramin kasuwanci. Duk da cewa sana’ar tana da ƙanƙanta a idon mutane da yawa, amma tana da riba”.
Bugu da ƙari, Umar Bashar, ɗaya daga cikin ’yan kasuwa daga Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi da ke sayar da shinkafa da wake a kasuwar ya ce, “duk da hauhawar farashin kayan abinci da ake ci gaba da samu, muna ci gaba da samun riba. Daga safe zuwa maraice, ina iya sayar da buhun shinkafa tsakanin buhu biyu zuwa uku da buhun wake sannan in samu tsakanin N10,000 zuwa N20,000 a matsayin ribata. A matsayina na ɗan ƙauye, wannan adadin ya isa in kula da iyalina na tsawon mako guda ko ma fiye da haka.”
Wakilin Aminiya ya lura cewa, duk da muhimmancin da take da shi ga masu ƙaramin ƙarfi da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Bauchi, kasuwar C da C na nan a wani wuri na wucin-gadi kuma a filin Allah, wato a sararin subahana ake gudanar da ita, ba ginin shaguna ko rumfuna, ba tsaro kamar ofishin ’yan sanda da kuma ɗakin shan magani.
An kuma lura cewa, babu banɗaki a cikin kasuwar ko kusa da kasuwar, lamarin da ke tilasta wa ’yan kasuwa da kwastomomi su riƙa yin fitsari da bayan gida a fili duk lokacin da suka matsu.
Da yake magana kan yanayin kasuwar, Sakataren Ƙungiyar C da C, Ibrahim ya ce, “kamar yadda kuke gani, C da C kasuwa ce ta wucin-gadi. Muna yin kasuwanci a sarari, ba kamar sauran kasuwanni a cikin jihar da ke da tsari na dindindin ba. Za mu yi farin ciki, idan gwamnatin jiha ta zo, ta taimaka mana. Za mu yi farin ciki, idan gwamnati za ta iya samar mana da wurin zama na dindindin da gine-gine har ma da jari don bunƙasa kasuwancinmu.
Kasuwar tana ba da gudummawa sosai ga tattalin arzikin jihar, kuma a lokacin da gwamnati ta inganta yanayinta, za a samu ƙarin kuɗaɗen shiga daga gare ta.”