✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar baje kolin Jihar Katsina za ta bambanta da ta baya

Majalisar ‘Yan kasuwa ta Jihar Katsina ta ce kasuwar baje kolin wannan shekara za ta bambanta da sauran na baya. Shugaban Majalisar Alhaji Abdurrashid Salisu…

Majalisar ‘Yan kasuwa ta Jihar Katsina ta ce kasuwar baje kolin wannan shekara za ta bambanta da sauran na baya.

Shugaban Majalisar Alhaji Abdurrashid Salisu Danbedi ya shaida wa Aminiya haka a ofishin majalisar da ke cikin garin Katsina. Shugaban ya ce kasuwar baje kolin karo na 18 da za’a bude ranar Laraba mai zuwa, a filin kasuwar na din-din-din da ke babban birnin jihar, za ta fi ba da fifiko akan sha’anin kayan amfanin gona.
Taken kasuwar na bana shi ne “Bunkasa kananan masana’antu.” Kasuwar ta shirya abubuwa daban-daban domin ba masu kananan masana’antu damar baje kolin kasuwancinsu. Shigaban ya ce sun kuma gayyato jihohin Kano da Kaduna da Sakkwato da Zamfara da kuma Babban birnin Tarayya Abuja da sauransu.
Har ila yau, ya ce “mun gayyato bankuna,ma’aikatun gona da sauran wasu cibiyoyin kasuwanci da dama”. Kamar yadda shugaban ya ce, daga cikin tsare-tsaren kayatar da kasuwar baje kolin harda gayyato wasu cibiyoyin kula da namun daji domin kawo namun daji da za su nishadantar da masu cin kasuwar,hatta da masu wasan kwaikwayo ba’a barsu baya.
Alhaji Abdurrashid ya ce, duk da cewa kasuwar baje kolin ba ta kasa-da-kasa ba ce, “amma mun gayyato wasu ‘yan kasuwar daga jamhuriyar Nijar wadanda dama ana cinta da su da kuma Jakadun kasashen China da Turkiyya da Brazil da makamantansu duk mun gayyace su,” kamar yadda shugaban yace.
“Bugu da kari, kasuwar wadda aka tanadarwa kowace karamar hukuma fili da ranar da za ta gabatar da irinta ta hajar, suma masu kawo ababen sayarwa an yi musu tsari na fitar da wajajen nau’in kayan baje kolinsu waje daya, ba kamar a baya ba, inda za’a taras da masu sayar da kayan lantarki sun hade da masu kayan abinci, ”inji shi.
Kasuwar ta bana dai za ta kafa tarihin da za’a dade ana tunawa da shi, saboda Gwamnan Mai barin gado ne Barista Ibrahin Shema shi ne zai bude ta, yayin da kuma Gwamna Mai jiran gado Alhaji Aminu Bello Masari ne zai rufe ta.