✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwancin fina-finai: Sani Rainbow da Nura Hussaini sun yi muhawara kan kwamiti

Fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa, Alhaji Sani Rainbow da jarumi Nura Hussaini sun yi muhawara a sakamakon wani kwamitin inganta kasuwancin fina-finai da Shugaban Hukumar…

Fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa, Alhaji Sani Rainbow da jarumi Nura Hussaini sun yi muhawara a sakamakon wani kwamitin inganta kasuwancin fina-finai da Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’Abba Afakallah ya kirkiro.

Wannan kwamiti dai an danka shugabancinsa a hannun fitaccen furodusa kuma jarumi, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ne, inda kwamitin ya gudanar da taron farko mako uku da ya gabata.

dan kasuwar da kuma jarumin sun yi musayar yawun ne a wani zaure na WhatsApp mai suna Kannywood banguard a makon jiya.

A yayin musayar yawun Sani Rainbow ya zargi Afakallah da karya kasuwancin masana’antar fina-finai, yayin da Nura Hussaini ya mayar da martanin cewa shi Rainbow yana yada fina-finan badala, kuma ya fi so a bar shi ya rika taka doka. 

Rainbow ya ce “Na yi farin ciki da wannan kwamiti da aka nada, karkashin shugaba mai girma, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama, don saboda mun san jajircewarsa, to muna ganin za a gano bakin zaren.

“A halin da aka ciki yanzu, furodusoshi wadanda suke kashe miliyoyi suna manyan fina-finai, wato furodusoshi irinsu Nazifi Asnanic, Umar Uk da Abba Miko da Abdul Amart, wadansu su kai kasuwa, wadansu kuma su sayar mana manyan ’yan kasuwa, kuma a ci riba, kudaden da ake kashewa suna nunkawa wajen cin riba, duk irin wadanan furodusoshi da na ambata da ma wasu sun koma yin fina-finan gidan talabijin, a fita da dubu 600 a yi fina-finai uku, ana tunanin a  kai wa gidan talabijin ya saya Naira dubu 300, ko 500 shi ke nan an ci rba, to ka ga wannan masana’anta ta koma baya.” Inji Rainbow.

Ya ce sakon da yake so ya isar ga wannan kwamiti shi ne, “sai an cire son rai, an tabbatar da za a yi aiki tsakani da Allah, saboda mun tabbatar da irin wadannan mutane da aka sa irinsu Kabiru Maikaba da shi shugaba na wannan kwamiti, mun san mutane ne jajirtattu, masu yin aiki tsakani da Allah, to amma yadda labarai suka zuwa mana cewa akwai sa hannun shugaban hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, wato Afakallahu a cikin wannan kwamiti, in har akwai hannunsa, to tsakani da Allah babu wani aiki da wannan kwamiti zai yi, sai dai ya zauna ya yi surutun banza, kuma a ci baya, dalilin da ya sa na fadi wannan magana kuwa shi ne, duk halin da masana’antar nan take ciki a halin yanzu, to Afakallahu ne ya jefa ta a cikin wannan hali.”

Ya kara da cewa dalili kuwa shi ne, lokacin da ya amshi wannan hukuma ya same “mu da mu da furodoshinmu muna yin fina-finai da ba su yi kasa da miliyan biyu zuwa uku ba, kuma ana sayen wadannan fina-finai har miliyan hudu zuwa biyar, sai ya zo da son rai, son ran da ya zo da shi shi ne, sai ya kama satifiket din wannan ya rike, ya ce sai ya karya wane, ko sai ya daure wane.

“Ya same mu a wannan kasuwa tamu bisa wani tsari, kamar ni za ka iya samu ina da fina-finai shida zuwa bakwai, za ka iya samun Adam A Zango yana da fina-finai uku ko hudu, ko Falalu dorayi yana da fina-finai takwas a hannunsa, duka ana talla, burinmu shi ne, za a ci gaba da tallata su a hankali, ana kawo kananan fina-finai ana maleji, lokacin da kaka ta bude, daga Janairu zuwa Afrilu lokacin kasuwar fina-finai take ja, an sayar da kayan gona, mutanen kauye daga sauran jihohi na zuwa sayen fina-finai.” Inji shi.

Ya ce a lokacin kaka suke rige-rigen sakin fina-finai, domin a samu kudaden da za a mayar wa furodusoshi, don su koma lokeshan, a dauki sabbin fina-finai kafin wata shekarar ta sake biyo wa baya.

Ya ce, to a lokacin da Afakallahu ya zo, a  lokacin da ya kamata a saki fina-finai, sai ya kama satifiket din wannan ya rike, a yi ta rigima, a ki sake fina-finai, har lokacin da kasuwa ta ja baya, lokacin da aka sake su kuma ruwa ya sauka, don haka komai kyan fim, ba za a kalle shi yadda ya kamata ba, to haka Afakallahu ya yi ta yi har ya karya ’yan kasuwa.

“Alal misali ni, ina da satifiket din fim din ‘Indon kauye’ da wani fim mai suna ‘Rumfar Shehu’, na sayi fim din akalla kusan Naira miliyan biyar da rabi, Afakallahu ya kama satifiket din fim din ‘Rumfar Shehu’ ya rike, aka yi ta rigima sai Fabrairu aka samu aka kawo fim din  kasuwa, lokacin da zan saki fim din ‘kasata’ da ‘Gamu Nan Dai’ wanda na saya a wurin Ali Nuhu, Afakallahu ya kama satifiket dinsu ya rike, ya ki ya saki fina-finan har sai da aka yi ta rubuce-rubuce, ko da ya sake su ruwa ya sauka, inda na yi asarar kusan Naira miliyan 10.” Inji Rainbow. 

Ya jaddada cewa ba shi kadai ba ne kawai ya yi asara, domin furodusoshi irinsu Shazali Kamfa da Aminu ArRahuz duk sun yi asara, inda yanzu kasuwar ta karye, kowa ya ja da baya, “A fada wa Afakallahu idan bai cire son rai ba, to ba za a je ko’ina ba, ba za a ci gaba ba.”

A lokacin da Nura Hussain yake mayar da martani ne ya ce, “Sani Rainbow na ji abin da ka ce, kuma gaskiya bayaninka babu abin da yake nuna wa face son rai, dalili shi ne na fuskanci kai mutum ne mai gadara, kuma kai mutum ne mai nuna babu wanda ya isa, shi ya sa kake da dabi’ar karya doka.”

Ya ce, a baya kafin zuwan Afakallahu, a lokacin (Ahmad) Beli na shugaban hukumar tace fina-finai, Rainbow ya saki wani fim mai suna ‘dakin Amarya’, ba tare da an yi masa izini ba, ba tare da an ba shi satifiket ba. 

“Har aka kai ka kotu, wannan rikicin idan ka manta, shin Afakallah ne ya ja maka? Sannan kana wata magana a cikin (record) dinka, akwai takardu da ka rubuta a cikin fayil dinka na neman alfarma, na nan ka yi laifi, na  nan kana neman afuwa, har aka zo fim din ‘Ana Wata Ga Wata’, wanda babu abin da yake cikin fim din sai kalaman da kai kanka ba za ka so a ce sun shiga cikin gidan ’ya’yan Musulmi ba, saboda akwai kalaman da suka shafi batsa.” Inji Nura Hussain. 

Ya tambayi Rainbow cewa, yana ganin a debi kudi a yi fina-finan da za su gurbata tarbiyya shi ne ya kamata? “Shi Afakallahu ya ba ka dama sannan ka ce ya hana ka sakin abin da kake so ka sake. Ba ka yi wa Afakallu adalci ba, da ni da kai da Ali Nuhu idan ba ka manta ba, ka nemi alfarma, Ali Nuhu ya kira Afakallahu, muka zo muka zauna a wani (Restaurant) muka ba Afakallah hakuri, a kan ya yi hakuri ya yafe maka abin da ka aikata.”

Nura Hussain ya kara de cewa kada Rainbow ya manta bai taimaki fim ba, fim ne ya taimake shi, domin babu wani abu da ya dauko, ko bulo ka sumunti wajen gina wannan sana’a, zuwa kawai ya yi ya more ta, kuma kada ya manta gwamnati ta dauki miliyoyin kudi ta ba ’yan fim, kuma Rainbow yana ciki.

“Kuma idan ka yi magana cewa wadansu ne suka karya ’yan fim, ko suka karya kasuwanci, ko Afakallahu ne, wannan ba gaskiya ka fada ba, tun da aka kafa hukumar tace fina-finai, ba a taba samu mutumin da ya taimaki ’yan fim kamar irin Afakallahu ba, ya samar da ofisoshi, ya saya musu babura, inda duk ba ka zata ba ana shiga, ana yaki da masu satar fasaha, shi ya horar da  ’yan fim 450 kan harkar inganta daukar fim da kasuwacinsa, inda aka dauko a kowane bangare kama daga fitowa a fim da shiryawa da bada umarni da fitila da kwalliya da sutura da sauransu.” Inji shi.

Ya ce Afakallah ne ya sa Gwamna (Ganduje) ya samar da kasuwar ’yan fim, inda take cikin kasafin kudi na 2018, kuma ba a taba yi ba.

“(Afakallah) yana kokarin ganin an kawo kudi don bunkasa tattalin arzikin masana’antar fim, me ya sa ba ka fadin wannan aikin alherin ba?  Afakallahu ya kuma kafa wannan kwamitin ne, ya danka shi ga Iyantama saboda nagartarsa don ganin an inganta wannan sana’a. Yanzu har Rainbow ya manta alkhairai da Afakallahu ya samar kasa da shekara uku yana kan mulkin hukumar?” Inji Nura.

A lokacin da Sani Rainbow yake mayar da martani ne ya ce, “Malam Nura Hussaini na ji maganganunka, ka ce masana’antar fim iskota na yi bayan an gina ta, na samu arzkin da ke cikinta, wannan magana taka da ka fada haka ne, koda na zo masana’antar na same ta an gina ta, na shigo ciki na samu arziki a cikinta, kuma ina godiya ga Allah.”

Ya ce, maganar ba da gudunmuwa a masana’antar fim ba zai yi alfahari ba, lokaci ne ya yi da zai fada, kuma Allah Ya san niyyarsa ta fito da wannan magana.

“Duk mutanen da muka yi mu’amala da su, furodusoshi da ’yan kasuwa nake so a je a tambaya wace gudunmuwa Alhaji Sani Raibow ya bayar a wannan masa’ananta. Duk mutumin da na sayi fim a gunsa ko na sayar masa da fim dinsa, to na biya shi babu kyashi.

“Wadanda suka gina muhalli da wadanda suka sayi motoci da aure saboda mu’amalar kasuwancin da na yi da su suna da yawa. Ka ga kuwa ba za a ce ban bayar da gudunmuwata ba duk da na iske an kafata.” Inji shi.

“Dangane da maganar fim din ‘dakin Amarya’, kamar yadda ka sani ba ni na yi furodusin dinsa ba, sayensa na  yi, kuma ba ni aka kai kotu lokacin Beli ba, sannan maganar cewa ina yada fina-finan badala, wannan magana taka maganar banza ce, domin duk fina-finan da nake yi za ka gansu bisa doron addini da kuma al’ada.”