✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwanci ya fi aikin gwamnati rufin asiri – Abban dan Small

Wani dan kasuwa ya bayyana cewa harkokin kasuwanci sun fi rufin asiri idan aka kwatantasu da aikin gwamnati.dan kasuwar mai suna Abban dan Small, wanda…

Wani dan kasuwa ya bayyana cewa harkokin kasuwanci sun fi rufin asiri idan aka kwatantasu da aikin gwamnati.
dan kasuwar mai suna Abban dan Small, wanda aka fi sani da Mai Kayan Makka ya bayyana cewa  lokacin da ya shiga harkokin kasuwanci ya fara ne da shago guda, amma a yanzu yana da manyan shaguna guda biyar domin ba da tasa gudunmawa wajen magance matsalar zaman kashe wando a tsakanin matasa.
Ya kara da cewa “kasuwanci wani abu ne da ke bukatar hakuri da juriya sannan kuma mutum sai ya rage dogon buri kafin ya samu ci gaba mai ma’ana a rayuwa,” inji shi.
“Lokacin da na fara kasuwanci ba ni da wani jari mai yawa, amma sakamakon yadda na yi hakuri da kadan gashi yau ina zuwa har kasashen waje domin saro kayayyaki irin su Takalmi da jallabiya ta maza da ta mata,” inji shi.