✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwanci tsakanin Najeriya da China ya samar da Dala biliyan 18

Jakadan kasar China a Najeriya, Gu diaojie ya ce hada-hadar kasuwanci da ke tsakanin kasarsa da Najeriya daga watan Disamba, 2014 zuwa Fabrairu 2015 ta…

Jakadan kasar China a Najeriya, Gu diaojie ya ce hada-hadar kasuwanci da ke tsakanin kasarsa da Najeriya daga watan Disamba, 2014 zuwa Fabrairu 2015 ta kai ta kimanin Dala biliyan 18.1.
Jakadan ya ce hakan ya nuna an samu karuwar kashi 33 cikin 100 daga Dala biliyan 11 da digo bakwai a shekarar 2013.
Ya yi furucin ne a wata liyafa da aka shirya don murnar zuwan sabon jirgin ruwan yaki wacce aka gudanar a karshen makon da ya gabata a yankin bictoria Island da ke Jihar Legas.
Jakada Gu wanda babban jami’in ofishin jakadancin kasar China a Najeriya mai suna Mista Liu Kan ya wakilta ya bayyana cewa an samu karuwar bunkasar kasuwancin ne, saboda kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ya ce “Muna da alaka ta kusa da kasar Najeriya tare da hadin kai a bangarori da dama wadanda suka hada ta fuskar ayyukan soja, kuma muna amfanar juna. Bukatar da gwamnatin tarayya ta nuna na ba kamfanin kasar China kwangilar kera jirgin ruwa na yaki ya kara bunkasa alakar kasuwancin da ke tsakaninmu.”
Saboda haka ya ce wannan ya sanya kasar China ta zama kasar da ta fi kowace kasa shigar da kayayyaki a kasashen Afirka.
A nasa jawabin, Shugaban rundunar sojan ruwa, Usman Jibrin ya ce sayo jirgin ruwan zai kara bunkasa yakin da sojojin ruwa suke yi da barayin kan teku da kuma barayin mai.
“Samun wannan jirgin yaki zai karfafa gwiwar sojojinmu su gudanar da ayyukansu da doka ta dora musu kuma zai bude sabuwar kafa dangane da dangantaka tsakanin Najeriya da kasar China. Samar da kyakkyawan tsaro shi zai ba Najeriya damar bunkasa tattalin arzikinta bisa la’akari da dogaron da ta yi da teku. Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya goyi bayan tsarin fasali da bunkasa rundunar sojojin ruwa tun daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2020.” Inji shi
Ya kara da cewa zuwan jirgin ruwan ya tabbatar da kokarin da shugaban kasa yake yi na karfafa rundunar sojin ruwa Najeriya ta yadda za ta iya tunkarar kowace barazana.
Ya bayyana cewa bayan kaddamar da jirgin za a tura shi wurin da ya zai yi aiki tare da wani jirgin ruwan da Najeriya ta sayo daga kasar Amurka mai suna NNS Okpabana don yin aiki gadan-gadan a iyakokin ruwan Najeriya.