Wani rahoton da wata kungiya mai zaman kanta mai suna CODE ta fitar ya gano cewa kimanin kaso 80 cikin 100 na asibitocin Najeriya ba su cika ka’idar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA) ba.
Rahoton na CODE dai ya mayar da hankali ne a binciken da kungiyar ta gudanar a Jihohi 15 na Najeriya.
- Za a rataye mutumin da ya kashe matarsa da danta a Adamawa
- Har yanzu NCC ba ta sabunta lasisin kamfanin MTN ba
A cewar wata jami’ar kungiyar, Khadijah Muhammad Abdulhameed a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a garin Jos ranar Litinin, sun tattara alkaluman ne bayan shafe wata uku suna tattara bayanai a kai.
Ta kuma ce da cewa binkicen ya sami tallafi daga gidauniyoyin Conrad Hiltop da Skol.
Ta ce Jihohi shida da suka zaba wajen gudanar da rahoto sun fito ne daga sassa daban-daban na Najeriya, inda suka nuna cewa biyu daga cikin kowanne asibitin sha-ka-tafi ba su da wutar lantarki inda suke haska aci-bal-bal da cocila.
Kazalika, rahoton ya gano cewa kaso 30 cikin 100 na asibitocin kuma ba da ruwan sha mai tsafta inda suke dogaro da ruwan rijiya ko na sama wajen amfani
Jami’ar kungiyar ta kuma ce, “Bincikenmu ya nuna cewa da yawa daga cikin asibitocin sha-ka-tafin suna karbar kasa da kunshi 10 na allurar rigakafin COVID-19.
“Hakan ya janyo tambayoyi akan mafi yawan yankunan da yawanci suke da kimanin mutum 1,000 a kusan kaso 90 cikin 100 na asibitocin,” inji ta.
Da yake nasa jawabin a wajen taron, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na Jihar, Livinus Muapkwap ya ce gwamnatin Jihar na yin duk iya kokarinta wajen dakile matsalolin lafiyar da ke addabar Jiyar.
Kungiyar ta ba da shawarwari ga hukumar da ta kirkiri kwamitin sa’ido wanda zai rika kula da kowane asibiti don tabbatar da ingancinsa.