Wani rahoton Cibiyar Kwararru Masu Bincike da Bin Diddigi ta Najeriya (CIFIPN), ya gano cewa akalla kaso 75 cikin 100 na kasafin kudin gwamnatoci a dukkan matakai na salwanta ne a bangaren cin hanci da rashawa.
Shugaban cibiyar, Dokta Enape Victoria Ayishetu, ce ta bayyana hakan yayin zantawarta da manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
- Mene ne amfanin Jigida da warwaron kafa ga mata?
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Sayen Aikin Gwamnati A Najeriya
A cewarta, za a ci gaba da samun matsalolin matukar ba a dauki kwararan matakai wajen toshe almundahanar ba.
Ta ce da kyar ake iya aiwatar da kyawawan manufofin kasafin kudin a zahiri, ta yadda talakawa za su gani a kasa.
Ayushetu ta alakanta hakan da cin hanci da rashawar da suka yi wa Najeriya katutu tsawon lokaci saboda rashin bincike tare da hukunta masu karkatar da kudaden.
Shugabar cibiyar ta ce, “Kaso mai tsoka na albarkatun Najeriya a kodayaushe na karewa a damfara, cin hanci da rashawa. Wannan ne ainihin yanayin da Najeriya ke ciki.
“Zunzurutun kudaden da ake yin kasafinsu a kowace shekara ba su dace da abin da ake gani yanzu a kasa ba, musamman na halin da mutane ke ciki.
Ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya rattaba hannu a kan kudurin dokar cibiyar na shekarar 2021.
Dokta Enape ta ce yin bincike da kuma bin diddigi za su taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arziki da yaki da rashawa.