Mene ne bambanci tsakanin ajujuwan jinin nan na A da B da O? Shin mutum mai A zai iya komawa ajin O ko B?
Amsa: Ba dukanmu ne ajujuwan jinin jikinmu suka taru suka zama iri daya ba, duk da cewa a ido za a iya ganin na kowa baki-baki ko jazur. A boye a jikin jajayen kwayoyin jini na kowa akwai wasu sinadarai da sukan iya bambanta jinin wane da wane, ko su yi kama da na wane, wadanda ido ba ya gani. Wannan bambanci shi kan sa ko jinin mutane masu jini mabambanta ne ya zuba a kasa, ba za su hadu ba, ballantana a jiki, kamar dai yadda ruwan koguna biyu ba sa haduwa ko da a wuri daya suke. Idan mabmbantan jini suka hadu ko a kasa ne, nan da nan za a ga sun dunkule wuri guda ko sun cure (wato agglutination).
A 1900 wani Bature mai binciken kwayoyin halittun jini Karl Landsteiner ya gano cewa akwai wadanda suke da jini daban da wadansu, wadanda ya raba aji-aji zuwa ajujuwan da kike tambaya, na A da B da O. Wato akwai mutane masu wasu irin sinadarai a kan jajayen kwayoyin jininsu da suka ba harafin A. Akwai kuma mutanen da suke da wasu iri daban da na A, wadanda suka ba harafin B. Akwai kuma wadanda ya lura a kan kwayoyin jininsu suna dauke da duk sinadarai masu kama da A da B, wadanda ya ba sunan haruffan AB. Sai kuma ya lura akwai ma wadanda a jikin kwayoyin jininsu babu wasu sinadarai irin wadancan ko daya, wadanda ya ba sunan harafin O ko sifili, wato ba su da komai. Idan kika lura ajujuwa hudu ke nan ba uku ba kamar yadda kika rubuto. Ajujuwan kuwa su ne ajin A da B da na AB da na O.
Bayan wasu ’yan shekaru kuma sai ya sake gano cewa a cikin wadannan ajujuwa hudu akwai bambance-bambance har ila yau, inda ya gano akwai wani sinadarin kuma, wanda wadansu suke da shi, wadansu kuma ba su da shi. Wannan sinadari shi ya lakaba wa harafin D. Dangane da ko a akwai kowane harafi a jinin mutum ko babu shi ne ake ba da alamun + ko – dangane. Shi ya sa za ki ga wadansu an ce ajinsu AB+ ko AB- da sauransu. Akwai sauran sinadarai a jikin kwayar jini da suka bambanta daga wani zuwa wani, amma wadannan da aka lissafa su ne muhimmai, wadanda idan ma’aikacin lafiya ya san su ciki da bai, ba zai yi kuskuren hada jinin wani da na wani ba musamman a wurin karin jini da haihuwa, inda hada jinin wani da wani kan iya jawo salwantar rai.
Kamar yadda kika sake neman bayani ko mutumin da ke wani ajin jini kan iya rikidewa ya dawo na wani ajin, ana iya samu idan aka yi wa mutum dashen bargon kashi na wani daban, tunda a bargo ake haihuwar kwayoyin jini. Wato ke nan idan aka yi wa mutum mai ajin jini A dashen bargon wani mai ajin O, a hankali bayan shekaru mai ajin A din zai iya rikidewa ya dawo ajin O. Hakan ba ta yiwuwa idan kawai karin jini ne ba bargo ba. Wato idan aka kara wa mutum mai ajin B, jinin mai O ba zai rikide ya dawo ajin O ba.
Mene ne bambancin ciwon asma da COPD?
Daga Babangida A., Kano
Amsa: Ciwon asma karamin ciwo ne a kan COPD. Ciwon COPD na nufin dadadden ciwon huhu, wanda idan ya riga ya auku mutum ba ya da wani sakat, domin kullum tari da matsalar numfashi zai yi ta samu. Don haka idan mutum yana da ciwon huhu da ya dade a jiki zai iya zama COPD. Misali shi ne ciwon asma da ya dade ba a yi masa maganin da ya dace ba, wato idan ba a yawan bibiyar likita a karbi maganin kwantar da shi. Akwai ma COPD na masu shan sigari wanda ma shi ne na daya. Akwai na masu aiki a kura kamar yadda aka taba bayani, akwai ma na masu zama ko aiki cikin hayaki kamar masu tuya a bakin titi, ko mazauna yankunan masana’antu masu fitar da hayaki.
Ina da matsalar jin magana, mun je asibiti an ba ni na’urar kara jin sauti. To yanzu ba ma na iya ji kwata-kwata da ita, mun koma an sake cewa sai an sa wata na’urar a cikin kunne. To yaya abin yake?
Daga Saifu, Kaduna
Amsa: Ka san akwai irin tambayoyin da sai fa likitan fannin abin ne kadai zai iya yi maka bayani. Don haka ba a hurumin likitan iyali ko na jama’a irinmu wannan tambaya take ba. Abin da dai muka sani shi ne akwai na’urar kara sautin iri biyu, da ta waje da ta ciki. To watakila ta ciki din za a sa maka. Idan kana son karin bayani, shi likitan kunne za ka zubo wa duk tambayoyin abubuwan da suka shige maka duhu game da na’urar.
Wai da gaske naman ganda ba ya da wani amfani ga jikin dan Adam?
Daga Nasir Shehu, Sakkwato
Amsa: Eh, to ba za a ce ba amfani ba, tunda akwai kitse a jiki, wanda zai iya wa wadansu (masu neman kiba) amfani, ya iya yi wa wadansu (masu kiba) illa.
Ko ana iya daukar cuta a wurin fitsari na jama’a kamar a kasuwa ko tasha?
Daga H.S.Aliyu, Zaria
Amsa: kwarai kuwa, tunda wurin yakan yi wari da zarni da karni, wanda su kuma kwayoyin cuta abin da suke so ke nan, nan ne matattararsu. Don haka a bayan gida wanda ake biyan kudi ake tsabtace shi kamar gidan wanka da ba-haya ya kamata ko da fitsari ne a rika yi.
Wai shin amfani da madarar turare a fata tana da illa ne ko kuwa? Domin ni a jiki nake shafa shi ba a tufafi ba.
Daga Aliyu Jekanadu
Amsa: Eh, ai ka san turarukan iri-iri ne, akwai na shafawa a fata akwai na shafawa a tufafi. Na shafawa a tufafi za ka ga fesa shi ake yi. Na shafawa a fata za ka ga ba ya da abin feshi sai dan dutsen gogawa a fata. To haka ya kamata ka rika yi, idan kana so ka shafa a fata ka nemi na musamman na fata ba na feshi ba. Ba za a ce shi na feshin idan ka fesa a fata zai yi maka illa ba, amma ana ganin wadansu fatarsu za ta iya samun matsala da na feshi kamar kuraje da kaikayi da canjin launi.