Ministocin Harkokin Waje na Tarayyara Turai sun amince da dakatar da bayar da bizar shiga kasashensu ga ’yan kasar Rasha don nuna adawa da yakin da kasarsu ke yi a Ukraine.
Babban jami’in harkokin waje na kungiyar ta EU, Josep Borrell, ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Prague, ranar Laraba.
- Ina tausaya wa Shekarau kan komawarsa PDP – Buba Galadima
- Bayan umarnin Buhari, sojoji na samun nasara kan ’yan ta’adda
Ya ce matakin zai kunshi dakatar da yarjejeniyar bayar da bizar da ke tsakaninsu da Rasha ta shekarar 2007.
An sa haramcin ne saboda a hana duk ’yan Rashar da ke son shiga kowacce kasa a cikin Tarayyar ta Turai cikinn ruwan sanyi.
Bugu da kari, matakin na Tarayyar Turai na zuwa ne bayan shafe tsawon makonni mambobin da ke cikinta na bukatar a hana ’yan kasar bizar da wasu daga cikinsu suke bayarwa.
A cewar EU dai, sabon matakin zai sa tsarin neman bizar ya dada wahala, ya kara tsada sannan lokacin da ake jira kafin a same ta ya kara tsawo.