✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashe 7 da ake amfani da harshen Hausa bayan Najeriya

Harshen dai ya yi shura ta yadda ba iya Najeriya ake amfani da shi ba.

Hausa harshe ne da ya yi shura a Afrika musamman yammacin nahiyar, kuma ana hasashen mutane sama da miliyan 150 ne ke amfani da shi a matsayin harshen amfani na yau da kullum.

Harshen dai ya fi karfi a Najeriya, inda ya ke da adadin mutane masu yawa da ke amfani da shi a matsayin harshen uwa, amma da akwai wasu kasashen da su ma suke amfani da shi.

Ga wasu daga cikin wadannan kasashen:

1. Nijar

Jamhuriyar Nijar ita ce kasa ta biyu da ke da mutane masu dimbin yawa da ke amfani da harshen Hausa.

Kasar na da iyaka da Najeriya daga kudu, Libya daga Arewa maso Gabas da kuma Chadi daga gabas.

Ana hasashen akwai mutum miliyan 10 da ke amfani da harshen Hausa a kasar.

2. Chad

Kasar na da dubban mutane da ke amfani da harshen na Hausa, kuma tana Arewa da tsakiyar nahiyar Afrika. Kasar na da adadin mutane miliyan 16 da ke rayuwa a cikinta.

3. Ghana

Kasar na amfani da Turanci a matsayin harshen mu’amala na yau da kullum, amma akwai mutane da yawa da ke amfani da harshen Hausa a kasar.

Ghana dai na tsakiyar Yammacin Afrika, kuma tana da mutane sama da miliyan 30 da ke rayuwa a cikin kasar.

4. Togo

Togo kasa ce da ke yammacin nahiyar Afrika, tana da adadin mutane miliyan takwas da ke rayuwa a cikinta kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana a 2020.

Kuma akwai wasu yankuna na kasar da ake amfani da harshen Hausa sosai.

5. Benin

Kasa ce da ke yammacin Afrika kuma tana amfani da Faransanci a matsayin harshe na musamman.

Amma wasu yankuna na kasar na amfani da harshen Hausa da al’adun Hausawa.

6. Kamaru

Harshen da ake amfani da shi a kasar Faransanci da Turanci ne, kazalika akwai yankuna masu yawan gaske da ke amfani da harshen Hausa.

Hakan yasa ake kiran wasu unguwanni da sunayen Hausawa; kamar Zangon Hausawa da sauransu.

7. Sudan

Hausa na daya daga cikin harsunan da aka fi yi a Sudan.

Kasa ce mai harsuna da yaruka masu yawa, amma an fi amfani da Larabcin Sudan, Turanci da kuma harshen Hausa.

A wasu yankuna na kasashen da ake amfani da harshen Hausa, a kan samu sunayen unguwanni, al’adu wasu lokuta har da sarautar gargajiya irin ta malam Bahaushen Najeriya.