✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashe 6 da suka fi iya Turanci a Afirka

Turanci ya zame wa wasu kasashen Afrika harshen mu'amalar yau da kullum.

Harshen Turancin Ingilishi dai ya samo asali ne daga Ingila da wasu kasashen Turai, kuma shi ne harshen da aka fi yarawa a fadin duniya.

A Afirka kuwa akwai kasashe da dama da suka mayar da Turancin Ingilishi harshen mu’amalarsu ta yau da kullum, tamkar harshen uwa a gare.

Ga kasashe shida daga cikinsu:

1. Uganda: Kasa ce mai girman gaske a Gabashin Afirka ta yi fice sosai wajen kwarewa da iya Turanci Ingilishi tamkar nasara.

Allah Ya albarkaci Uganda da dukiya mai tarin yawa da ababen more rayuka. Tana da tsaunuka da dazuka hade da dabbobin daji irin su kakuman dawa, birai da sauran dabbobi.

2. Afrika Ta Kudu: A Kudancin Nahiyar Afirka, kuma ita ce ta biyu wejan iya harshen Ingilishi a Afirka.

Kasa ce mai kabilu da yawa amma tana da manyan yare guda 11 da suka fi shahara. Amma Turanci ya mamaye kasar sakamakon juyin juya hali da mulkin mallaka da Turawa suka yi wa kasar.

3. Najeriya: Ita ce kasa mafi yawan al’umma a Afirka baya ga dimbin albarkatun karkashin kasa da suka hada da man fetur da kasar noma gami da ma’adanai irin su zinare da tagulla da dabbobi da namun daji da koramai da sauransu.

A Najeriya kabilu da dama sukan mayar da Turanci tamkar harshen uwa kuma da Turanci ake mu’amala ta yau da kullum a dukkanin ma’aikatun gwamnati da harkokin ofis.

4. Kenya: Kasa ce da ta yi fice wajen yawan wararen yawon bude ido musamman gandun dabbobi da dazuka. Mutanen Kenya na alfahari da tarihinsu da al’adunsu.

Turanci ya kasance harshen da ake yarawa a tsakanin kabilu mabambamta a Kenya. Hakan ya sanya mutane yin mu’amala cikin sauki da juna.

5. Zambiya: Kasa ce mai cike da tarihi da al’adu sannan mai tarin kabilu kamar Najeriya, amma akwai manyan kabilu a kasar irin su Nyanja da Bemba da Lozi da Kaonde da Lunda da kuma Tonga.

Kasar ta yi fice wajen amfani da harshen Turancin Ingilishi wajen mu’amalar yau da kullum a makarantu da kasuwanci  harkar siyasa da sauransu.

6. Ghana: Ita ma kasa ce mai tarihi da al’adu da yawa. Kusan kowa a Afrika ya san yadda kasar ta yi gogayya wajen amfani da Turancin Ingilishi a matsayin harshen da ake mu’amala a tsakanin kabilun kasar.