✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashe 5 na son karbar bakuncin gasar AFCON 2027

Rashin wadatattun ababen more rayuwa na filin wasa ya kasance matsala ga galibin kasashen.

Kasashen Kenya da Tanzaniya da Uganda sun kaddamar da wani shiri na hadin gwiwa kan neman karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2027.

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta ce ta samu tayin karbar bakuncin gasar daga kasashen uku tare da tayin Aljeriya da Botswana da Masar.

A cikin watan Disamba ne gwamnatin Kenya ta amince da kudirin majalisar ministocin kasar na mara baya ga yunkurin shiga gasar, tare da wasu makwabtanta guda biyu cikin masu neman karbar bakuncin gasar.

Gwamnatin ta ce, hakan zai taimaka wa kungiyar kwallon kafa ta Harambee Stars, wajen cimma burinsu na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya a karon farko a shekarar 2030.

Ministan wasanni na kasar Kenya, Ababu Namwamba ya ce ya tattauna da takwarorinsa na Uganda da Tanzaniya, inda ya kara da cewa suna shirin kafa kwamitin hadin gwiwa ka shirin karbar gaar.

Rashin wadatattun ababen more rayuwa na filin wasa ya kasance matsala ga galibin kasashen gabashin Afirka, abin da ya tilastawa kungiyoyin kasa buga wasannin nahiya a waje.

A watan Satumba ne CAF za ta bayyana sunan kasar da zata karbi bakuncin, da kuma inda za a gudanar da gasar shekarar 2025, bayan da aka hana wa Guinea mai masaukin baki ‘yancin karbar bakuncin gasar a watan Oktoban da ya gabata.